Yan ta'adda
An kashe fitaccen kwamandan ’yan bindiga Jankare a rikici da abokan ta’addanci a yankin Dutsenma, jihar Katsina, bayan sabani kan sarauta da hare-hare.
Sabon shugaban sojin saman Najeriya, Sunday Kelvin Aneke ya bayyana cewa zai kai hana 'yan ta'adda sakat a Najeriya ta yadda za su gagara zama su kitsa kai hari.
A labarin nan, za a ji cewa rundunar yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa mutanen da aka gani da miyagun makamai ba 'yan ta'adda ba ne kamar yadda aka yada.
Sabon hafsan sojojin kasan Najeriya, Manjo Janar Waidi Shaibu, ya sha alwashin ragargazar 'yan ta'addan Lakurawa da ke kai hare-hare a yankin Arewaci.
‘Yan bindiga sun kai mummunan hari a Na’alma da ke karamar hukumar Malumfashi a Katsina, inda suka kashe mutane da dama yayin sallar Asubahin yau Laraba.
'Yan bindiga sun kakabawa wasu mutane a yankin Bazar na jihar Sokoto harajin N15m. Sun bukaci a sanar da gwamna domin kawo musu dauki kan halin da suke ciki.
Dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a Borno. Sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda tare da kwato makamai.
A labarin nan, za a ji cewa rundunar sojojin kasar nan ta yi asarar Janarori kimanin 500 daga zamanin Muhammadu Buhari zuwa na Bola Ahmed Tinubu.
Fasto Ezekiel Dachomo daga jihar Plateau ya ce idan an sace shi, kada a biya fansa, yana mai cewa jinin sa zai haifar da yaki na ’yantar da Kiristoci.
Yan ta'adda
Samu kari