Yan ta'adda
'Yan ta'addan kungiyar ISWAP sun sake kai hari kan wani sansanin sojoji a jihar Borno. 'Yan ta'addan sun yi amfani da jirage marasa matuka wajen kai harin.
Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu miyagun yan Boko Haram bayan an shafe kwanaki ana fakonsu da suka kai harin da ya shafe rayukan bayin Allah.
Dakarun sojojin Najeriya sun gano gawar wani kwamanda da sojoji 7 da 'yan ta'addan Boko Haram suka yi wa kisan gilla a Damasak; an kwashe su zuwa Maiduguri.
'Yan sandan Zamfara sun kama Mustapha Mohammad da abubuwan fashewa 954 a motarsa; ana zargin na 'yan bindiga ne domin kera bama-bamai a ranar 27 ga Janairu, 2026.
Wani shahararren jagoran 'yan bindiga da ke kira, Abdullahi Lantai ya mutu a Katsina wanda aka ce yana daga cikin masu son ganin an yi sulhu da gwamnati.
'Yan ta'addan ISWAP dauke da makamai sun kai harin kwanto bauna kan dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno. Harin ya janyo asarar rayuka da sace wasu sojoji.
A labarin nan, za a ji cewa Najeriya da Turkiyya sun samu fahimtar juna a kan yadda kasashen biyu za su yi amfani da bayanan sirri wajen yaki da ta'addanci.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin tura tsofaffin sojoji domin kare wuraren da ba gwamnati ke iko da su ba, don inganta tsaro da tattalin arziki.
Dakarun sojojin Najeriya sun bankado wani waje da ake kera makamai a jihar Nasarawa. An kama mutum daya yana kokarin guduwa ta kan bishiya a wajen.
Yan ta'adda
Samu kari