Yan ta'adda
'Yan bindiga sun saki bidiyon Sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa da suka yi garkuwa da shi a watan Yuli. Sarkin ya roki gwamnatin Sokoto ta kai masa dauki.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi nasarar kamata wata mata mai shekara 30 dauke da bindiga za ta kaiwa wani hatsabibin dan fashi da ya addabi jihar Katsina.
Mazauna angwan mai matasa a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa sun kwana da takaicin kisan wani matashin jami'in gwamnati ma kula da shirin Fadama III.
Sakamakon yawan kisan al'umma da ake a Gaza, makabartar Falasdinawa ta cika makil har an fara birne gawa a kan gawa kamar yadda wani ma'aikaci ya fada.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a karamar hukumar Dekina ta jihar Kogi. 'Yan bindigan sun hallaka wani babban basarake yayin harin.
Matafiya sun yi kicibis mugun gamo da 'yan ta'adda hanyar Gusau-Funtua, inda miyagun su ka ɗauke fasinjojin mota uku,tare da sace wasu a Unguwar Chida.
Wasu mutane sun kama wani mutum mai suna Musa dauke da kan wata mata a cikin buhu, ya ce yana sayar da sassan jikin dan Adam yayin da ake masa tambayoyi.
Kimanin mutane bakwai ne 'yan bindiga suka kashe a kauyen Sai da ke jihar Taraba. An ruwaito cewa wasu fusatattun matasa sun yi harin ramuwar gayya.
Wasu miyagun 'yan ta'adda sun yiwa dakarun sojojin Najeriya kwanton bauna a jihar Sokoto. 'Yan ta'addan sun hallaka sojoji hudu a harin da suka kai.
Yan ta'adda
Samu kari