Yan ta'adda
Miyagun 'yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya inda suka tafka ta'asa. Sun sace masunta masu yawa.
'Yan bindiga sun kai hari a gonakin Kwaga da Unguwar Zako a Birnin Gwari, jihar Kaduna, inda suka kona bukkokin masara. Manoma sun nuna damuwa matuka.
Wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya. 'Yan kungiyar Lakurawa na ayyukansu a jihohin Sokoto da Kebbi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban sabuwar kungiyar Lakurawa, Habib Tajje yana kokarin turawa Bello Turji sako kan ayyukan ta'addanci a jihar Sokoto.
A yayin da ake kuka cewa 'yan ta'addar Lakurawa sun fara karfi, gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu ya gana da ministan kudi, Mista Wale Edun kan ci gaban tattalin jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin da yan Gatawa sun kaure da yan ta'adda karkarshin jagorancin Bello Turji da safiyar yau Talata a yankin Bakin Gulbi Sokoto.
Gwamnatin jihar Kebbi ta tura tawaga wajen hafsun tsaron Najeriya domin hada kai wajen yaki da Lakurawa. Hafsun tsaro ya tabbatar da cewa za su yaki Lakurawa.
An samu matsala a Sakkwato bayan yan ta'addan Lakurawa sun gano lagon daukar wasu daga cikin matasan jihar a matsayin sababbin yan ta'adda domin karfafa ayyukansu.
Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya (NAF), sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda masu yawa a jihohin Zamfara da Kebbi. Sojojin sun lalata ma'ajiyar makamai.
Yan ta'adda
Samu kari