Jihar Osun
A karshe, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ta tare a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Osogbo bayan kammala gyaran da aka yi na tsawon lokaci.
Babbar kotun tarayya mai zama a Osogbo, bababan birnin jihar Osun ta umarci a garkame makusancin gwamna Adeleke a gidan yari kan tuhume-tuhume 10.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana irin matakan da ya soma ɗauka bayan samun bayanan ana shirin kai hare-hare makarantu da gonaki a Osun.
Wani fasto a jihar Osun ya halaka na gaba da shi a coci. Faston ya aikata wannan danyen aikin ne bayan wata takaddama ta barke tsakaninsa da marigayin.
Yayin da ake fama da tsadar kaya a Najeriya, Oba na Iwoland, Abdulrosheed Akanbi ya bukaci Shugaba Tinubu ya samar da hukumar kayyade farashin kaya.
Bayan kulle masallaci na tsawon shekaru biyar, malaman Musulunci a Inisa da ke jihar Osun sun shawarci Gwamna Ademola Adeleke kan shiga lamarin zaban limami.
Yarima Ibraheem Oyelakin ya zama sabon zababɓen Oba na masarautar Iree wata ɗaya kenan bayan Gwamna Ademola Adeleke ya tsige sarakuna 3 a jihar Osun.
Mambobin ƙungiyoyin fararen hula a jihohin Edo da Osun sun fantsama zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa a biranen Osogbo da Benin City yau Litinin.
An samu karin bayani yayin da mafarauta suka kashe zaki dan shekara 9 da ya kashe wani masanin fasahar dabbobi, Olabode Olawuyi a jami'ar OAU, jihar Osun.
Jihar Osun
Samu kari