"Musulmi Ne Ko Kirista": APC da PDP Sun Gwabza Kan Ainihin Addinin Gwamna, an Kawo Hujjoji

"Musulmi Ne Ko Kirista": APC da PDP Sun Gwabza Kan Ainihin Addinin Gwamna, an Kawo Hujjoji

  • Jam'iyyun APC da PDP sun gwabza kan halayyar Gwamna Ademola Adeleke kan ainihin addinin da ya ke bi
  • Jam'iyyar APC ta zargi gwamnan da bayyana kansa a matsayin Musulmi kuma Kirista a lokaci guda
  • A martaninta, jami'yyar PDP ta caccaki APC kan rashin madafa inda suka fake da neman sanin addinin gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Jam'iyyar APC a jihar Osun ta caccaki Gwamna Ademola Adeleke kan ainihin addininsa.

Jam'iyyar ta nuna damuwa kan yadda gwamnan ke ayyana kansa a matsayin Musulmi kuma Kirista a lokaci guda, cewar jaridar Punch.

An rasa addinin gwamna, PDP da APC sun caccaki juna
Jam'iyyun APC da PDP sun caccaki juna kan ainihin addinin gwamnan jihar Osun. Hoto: Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

Wane martani jami'yyar APC ta yi?

Shugaban jam'iyyar APC a jihar, Tajudden Lawal ya ce Adeleke ya saba doka wurin ayyana kansa a matsayin mai bin dukkan addinan biyu.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni sun ba hammata iska a taron karbar sababbin tuba daga PDP zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawal ya ce gwamnan ya na da 'yancin kasancewa Musulmi ko Kirista ko marar addini amma ban da kasancewa a dukkan addinan.

Ya zargi gwamnan da yin hakan domin yaudarar 'yan jihar yayin da ya ke neman kuri'unsu a zabe mai zuwa, cewar OsunDefender.

Jam'iyyar PDP ta kalubanci APC a Osun

A martninsa, shugaban jam'iyyar APC a jihar, Sunday Bisi ya kare gwamnan da aikata wani laifi kan lamarin.

Bisi ya ce APC a jihar ta rasa makama inda ta fake da neman sanin addinin gwamnan yayin da 'yan jihar ke mai da hankali kan ayyukan ci gaba.

Ya ce jam'iyyar APC ta nakasa jihar yayin da ta ke mulki inda Gwamna Adeleke ke kokarin farfaɗo da ita kan hanya madaidaiciya.

Gwamna Adeleke zai gina sansanin alhazai

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya aza harsashin ginin sansanin alhazai ga al'ummar Musulmi a jihar.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

Adeleke yayin wata laccar Ramadan da kungiyar NASFAT ta aka gudanar ya sha alwashin cewa zai samar da sansanin da zai dace da mahajjata a jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen fara jigilar alhazai zuwa kasar Saudiyya bayan ƙarin kudin kujera da hukumar ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel