Jihar Osun
Gwamnatin Osun ta nada Davido shugaban asusun tallafawa wasanni, domin janyo jari da inganta harkar wasanni, yayin da ake gyaran filin wasa na Osogbo.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya tabbatar da cewa jita-jitar da ake yadawa cewa ya gama shirin komawa APC mai mulkin Najeriya ba gaskiya ba ne.
Akalla ‘yan takara 14 daga jam’iyyar APC sun bayyana aniyarsu ta kalubalantar Gwamna Ademola Adeleke na PDP a zaben 2026 a Osun. Daga cikin su akwai Otunba Omisore.
Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, ya zargi APC da rashin kwarin gwiwa da danniya ga ‘yan adawa, yana mai cewa ADC za ta karbi mulki daga Tinubu a 2027.
Bayan tura shi gidan yari, gidajen sarauta da ke Aribile da Fagbemokun a garin Ipetumodu a jihar Osun, sun roƙi Gwamna Ademola Adeleke da ya cire Sarkin.
Dan majalisar tarayya daga jihar Osun, Hon. Wole Oke, ya karyata zargin cewa ganawarsa da jakadan Isra’ila na nufin adawa da kafa kasar Falasɗinu.
Al'umma a jihar Lagos sun shiga jimami bayan sanar da rasuwar tsohon jakadan Najeriya a Birtaniya, Dr Christopher Kolade wanda ya rasu yana da shekaru 92 da haihuwa.
Babbar Kotun Tarayya mai Zama a Osogbo, babbar birnin jihar Osun ta umarci sufeta janar na rundunar yan sandan Najeriya ya cafke shugaban INEC, Mahmud Yakubu.
Hukumar zabe ta INEC ta fitar da adadin mutanen da suka yi rajista a shirin mallakar katin zabe. Borno ta zamo ta daya yayin da Kano da Kaduna suke bayan Osun.
Jihar Osun
Samu kari