Nafi'u Bala: "Abin da Ya Hana Ni Amsa Gayyatar Kwankwaso"
- Daya daga cikin jiga-jigan ADC Nafi’u Bala ya bayyana cewa ba haka kawai ya yi fatali da kiran da Sanata Rabiu Musa Kwankwas ya yi masa ba
- Ya bayyana haka ne a dai-dai lokacin da jagoran Kwankwasiyya ya bayyana takaicin yadda Nafi'u Bala yaki amsa gayyatar da aka yi masa
- A zantawarsa da da Legit, Nafi'u Bala ya zargi Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran wadanda ke shugabancin ADC a yanzu da kaskantar da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Nafi’u Bala da ke da’awar shugabancin jam’iyyar ADC ya bayyana cewa ba haka kawai ya yi biris da kiran da Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi masa ba. Jagoran Kwankwasiyya na ƙasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana takaici game da yadda Nafi’u Bala ya ƙi halartar zaman sulhu da aka so a yi da shi.

Source: Twitter
The Cable ta ruwaito cewa bayan Sanata Kwankwaso ya koma ADC, ya nemi su gana da Nafi’u Bala da ke neman zama ƙadangare bakin tulu a tafiyar adawa da aka sabunta.
Nafi'u Bala ya magantu kan Kwankwaso
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana rashin jin daɗi tare da zargin Nafi’u Bala da jawo wa kowa matsala a tafiyar ADC.
Sai dai a zantawarsa da Legit ta wayar tarho, mai da’awar shugabancin na ADC ya bayyana cewa Kwankwaso da tawagar David Mark da ya shiga ba halastattun ƴan jam’iyya ba ne.
Ya ce:
“Shekara da shekaru sun riƙe mukamai amma ba su amfanar da al’ummar Arewa da Najeriya baki ɗaya ba."
“Maimakon su shigo ta halastacciyar hanya, sai su zo su ce su waye waɗannan da muka samu a ciki."
“Kamar yadda muka fara magana da su bisa ƙa’ida, za mu zo mu haɗu mu duba mece ce maslahar Najeriya, yaya za a yi a nada shugabannin jam’iyya, sai suka raina mu, suka nuna mana mu ba ƴaƴan kowa ba ne. Mu ba mu kai su bi mu ba, amma ƴaƴansu suna nan suna riƙe da mukamai kala-kala a ƙasa.”
Nafi’u Bala ya yi magana kan rikicin ADC
A tattaunawarmu da Nafi’u Bala ya bayyana cewa ya yi tsayin daka wajen ganin an bi doka da oda a cikin ADC domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Ya ce:
“Allah Shi Ya san gobe ba wani ba. Ko su zo su bi mu, su bi ƙa’ida, ko kuma ba za su yi jam’iyyar ADC ba."
“Rabi’u Musa Kwankwaso ya ayyana kansa cewa ya shiga jam’iyyar ADC, maimakon ya bi ta halastacciyar hanya, sai ya bi wata hanya da ba ta dace ba.”

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yana sane da cewa akwai rikicin shugabanci a ADC, domin akwai masu ruwa da tsaki daban-daban a jam’iyyar.
Nafi’u Bala ya ce kafin Kwankwaso ya shiga ADC ya kamata ya kira shi domin samun sahihan bayanai, amma maimakon haka ya ɗauki ɓangare.
Ya ce saboda haka babu amfanin ya zauna da Kwankwaso ganin cewa ya riga ya karkata zuwa wani ɓangare na jam’iyyar ADC, lamarin da ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar.
Nafiu Bala zai jawo wa ADC matsala
A baya, mun wallafa cewa jam'iyyar haɗaka ta ADC na ci gaba da fuskantar ƙalubale tun bayan haɗewa da tawagar jagororin adawa karƙashin Atiku Abubakar.
Tsohon ɗan takarar gwamnan Gombe a inuwar jam'iyyar ADC, Nafi'u Bala ya ce abin da haɗakar ƴan adawa ta yi tamkar fashin jam'iyya ne da ya saba ka'ida.
Ya ce shi da sauran 'yan ADC masu kishin jam'iyyar za su ƙalubalanci jagorancin David Mark a gaban kotu har sai an tabbatar masu da adalcin da suke bukata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


