Babbar Magana: An Gargadi Kwankwaso kan Zargin Kunna Rikici a Siyasar Kano
- Wata kungiya mai rajin kare zaman lafiya a Kano ta gargadi tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da nenam tada zaune tsaye
- Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa kungiyar ta yi magana ne bayan Amnesty International ta zargi Abba Kabir da kama 'yan adawa
- Kungiyar Kano Peace Coalition Group ta yi zargin cewa wasu 'yan Kwankwasiyya na amfani da kafafen sadarwa wajen tayar da fita a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Kungiyar Kano Peace Coalition Group ta zargi jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, da amfani da kungiyoyin matasa wajen haifar da rudani da hargitsi a jihar Kano.
Jagoran kungiyar, Datti Datti Tukur ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar cewa matasan Kwankwasiyya sun fara amfani da shafukansu wajen kai hare-hare ga manyan ‘yan siyasa.

Source: Facebook
The Guardian ta rahoto cewa Datti Tukur ya ce wadanda ake sun hada da gwamna Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Umar Ganduje, da kuma duk wanda bai amince da akidar Kwankwasiyya ba.
Zargin bata sunan Abba Kabir
Kungiyar ta yi nuni da wani lamari inda ta ce 'yan Kwankwasiyya sun bata sunan gwamna Abba Kabir Yusuf ta hanyar nuna shi cikin kayan mata ya yi kwalliya.
Datti ya kara da cewa, daya daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a wadannan ayyuka shi ne Abba Ibrahim Hussain wanda aka fi sani da Aiha, wanda ake zargin mashahurin mai amfani da yanar gizo ne kuma yana cikin Kwankwasiyya.
Magana kan Dan Bilki Kwamdan da wasu
Hakazalika, kungiyar ta ambaci batun wani Abdulmajid Danbilki Kwamanda wanda jami’an tsaro suka taba yi wa gargadi a baya bisa zargin ana amfani da shi wajen bata sunan gwamna Abba Kabir Yusuf da haifar da tashin hankali a jihar.
PM News ta rahoto cewa kungiyar ta ce duk da hujjoji da ake da su a kansa, ba a tsare Danbilki ba kuma ba a gallaza masa daga bangaren hukumomin tsaro ba.
Ta kuma bayyana cewa rahotannin da suka samu sun ambaci Samir Sani Hanga, dan Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Sani Hanga, wanda shi ma aka zarga da cin zarafi da bibiyar mutane ta yanar gizo.

Source: Facebook
Binciken kungiyar ya ce ya gano wani mai suna Abdullahi Aminu Warkal da ke Kwankwasiyya wanda aka ce jami’an tsaro sun taba gallaza masa kan sukar Abba Kabir Yusuf.
A kan haka kungiyar ta zargi Rabiu Kwankwaso da aiki da matasa masu amfani da intanet wajen tayar da zaune tsaye a kafafen sadarwa domin tayar da kura a Kano.
Amnesty ta gargadi Abba Kabir
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Amnesty International mai rajin kare hakkin dan adam ta yi zargin cewa gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf na murkushe 'yan adawa.
Amnesty ta yi ikirarin cewa an kama wasu mutane 'yan adawa a Kano bisa sukar gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu manufofin gwamnatinsa.
A kan haka kungiyar ta ce babu wanda ya fi karfin a soke shi, ko shugaban kasa ko gwamna, tana kira a girmama fadin albarkacin baki a jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

