Sanata Kawu Sumaila da Wasu Sanatoci 10 da Suka Sauya Sheka a Shekarar 2025

Sanata Kawu Sumaila da Wasu Sanatoci 10 da Suka Sauya Sheka a Shekarar 2025

A 2025 da ke dab da karewa, manyan 'yan siyasa ciki har da sanatoci sun rika canza jam'iyya daga wannan zuwa wata, galibi dai an fi samun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sauya sheka dai ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya, musamman idan aka fara harkokin tunkarar babban zabe.

Majalisar Dattawa.
Zauren Majalisar Dattawa a lokacin da sanatoci ke tsakiyar zama domin gudanar da ayyukansu na doka Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

APC ta samu kaso 2 cikin 3 a Majalisa

Daily Trust ta ce jam'iyyar APC mai mulki ta samu karin mambobi a Majalisar dattawa a wannan shekara ta 2025, har ta kai ga ta samu kaso biyu cikin uku na 'yan Majalisar,

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya ba ta damar zama jam'iyya mai rinjaye ta yadda za ta yi iya zartar da dokokin kasa ko da kuwa 'yan adawa ba su mara mata baya ba domin ta cika sharudda.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: 'Dan Majalisar Tarayya ya burma matsala, an kore shi daga YPP

Sanatocin da suka sauya sheka a 2025

A wannan rahoton, mun tattaro muku duka sanatocin da suka canza jam'iyya a 2025, ga su kamar haka:

1. Sanata Ned Nwoko

Sanata Ned Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a hukumance ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya tabbatar da hakan yayin da yake karanta wasikar da Sanata Nwoko ya aika wa Majalisa.

Da yake kafa hujja da rikice-rikicen cikin gida a PDP, Nwoko ya bayyana cewa halin da jam'iyyar ke ciki a yanzu yana barazana ga siyasarsa, wanda hakan ya sa ya yanke shawarar komawa APC.

Channels tv ta tattaro cewa sanatoci sun yi shewa da ihun murna yayin da aka raka shi zuwa ga bangaren masu rinjaye na majalisar dattawa.

2. Sanata Adamu Aliero

Tsohon gwamnan Kebbi kuma sanata mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Adamu Aliero ya sanar da sauya sheka daga PDP zuwa APC bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Da gaske an kama Wike a Faransa? Ministan ya fadi halin da yake ciki

A cikin wasiƙar da ya mika Majalisar Dattawa, Sanata Aliero ya bayyana cewa babban dalilinsa na sauya sheka shi ne rikicin cikin gida a cikin jam'iyyar adawa ta PDP.

Ya ce PDP ta rasa alkibla kuma ba za ta iya cika tsammani da muradan 'yan Najeriya ba, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Sanata Adamu Aleiro.
Sanata Adamu Aliero tare da sauran sanatocin Kebbi lokacin da suka sanar da shirinsu na komawa APC Hoto: Adamu Aleiro
Source: Twitter

3. Sanata Yahaya Abdullahi

A nasa bangaren, Sanata Yahaya Abdullahi, wanda ya sauya sheka tare da sauran sanatocin Kebbi ranar 13 ga watan Mayu, 2023, ya ce komawarsa APC tamkar ya dawo gida ne.

A wasikar da Akpabio ya karanta a zaman Majalisar Dattawa, Sanata Yahaya mai waliltar Kebbi ta Arewa ya ce:

"Ranka ya dade, na tuna a ranar 14 ga Yuni 2022 na fita daga APC kuma na yi murabus daga mukamina na shugaban masu rinjaye bayan rashin jituwar siyasa a jiharmu. Ina farin ciki cewa gwamna mai ci ya warware matsalar.
"Don haka ba ni da wani dalili na kin komawa APC, musamman tunda ni ɗaya ne daga cikin manyan wadanda suka tsara kafuwarta da kuma tushenta. A gare ni, komawata APC wani lamari ne na dawowa gida."

Kara karanta wannan

Ana wasan kora a PDP, tsagin Wike ya kori shugaban jam'iyya da wasu mutum 17

4. Sanata Garba Maidoki

Shi ma Sanata Garba Maidoki ya ce ya yanke shawarar fita daga PDP ne saboda rikicin cikin gida, tare da komawa jam'iyyar APC saboda manufofinta sun yi daidai da muradan mutanen mazabarsa ta Kebbi ta Kudu.

Ya ce:

"Rigingimun PDP ne duka kore ni kuma na fahimci manufofin APC suna da kyau, kuma ya dace mu hade kai gaba daya kan ajendar Renewed Hope, wacce nake da yakinin za ta amfani al'ummar mazabata."

5. Sanata Ekong Samson

Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Kudu a Majalisa Dattawa, Ekong Samson na cikin wadanda suka sauya sheka daga PDP zuwa APC a 2025, cewar rahoton The Nation.

Samson ya sanar da sauya shekarsa a hukumance ranar 23 ga watan Yulin 2025 lokacin da ya mika wasika ga Majalisar Dattawa. Ya kafa hujja da rigingimun da ake yi a PDP.

6. Sanata Etim Bassey

Haka zalika Sanata Etim Bassey mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Gabas ya bi sahun takwaransa, ya koma APC a wannan rana a Majalisar Dattawa, tashar Channels ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Bola Tinubu zai jagoranci babban taron jam'iyyar APC a Abuja

Tsohon Ministan Kwadago kuma tsohon gwamnan Anambra, Dr. Chris Ngige na cikin mamyan jiga-jigan da suka halarci zaman Majalisa domin shaida sauya shekar sanatocin biyu.

Sanata Etim Bassey
Sanata Etim Bassey yana jawabi a zaman Majalisar Dattawa Hoto: Senator Etim Bassey
Source: Facebook

7. Sanata Francis Fadahunsi

A wannan rana ta 23 ga watan Yuli, 2025, Sanata mai wakiltar Osun ta Gabas a Majalisar Dattawa ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC mai mulkin kasar nan.

Sanatan ya danganta ficewarsa da rikice-rikicen cikin gida da ke gudana da kuma rikicin shari'a da ba a warware ba a PDP tun bayan kammala babban zaben 2023, in ji rahoton Vanguard.

"Na yanke shawarar barin PDP ne bayan tattaunawa da mabiyana, iyalai da abokanan siyasa," In ji Fadahusi.

8. Sanata Olubiyi Fadeyi

'Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Osun ta Tsakiya, Sanata Olubiyi Fadeyiya bar PDP zuwa APC tare da takawaransa na Osun ta Gabas a watan Yuli, 2025.

A cewar rahoton Bussines Day, Fadeyi, ya yaba wa akidun APC da manufar Renewed Hope ta shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa hakan ya ja hankalinsa zuwa jam'iyyar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gwabza kazamin fada da ƴan bindiga a Abuja, an samu asarar rayuwa

"Babu wasa a wannan shawara da na yanke, ina ganin ya zama dole na yi hakan saboda rikicin cikin gida, shari'o'i daban-daban, da kuma rashin shugabanci a PDP," in ji shi.

9. Sanata Kaila Dahuwa Samaila

PDP ta sake samun koma baya a majalisar dattawa yayin da Sanata Kaila Dahuwa Samaila, mai wakiltar mazabar Arewacin Bauchi, ya koma jam'iyyar APC.

This day ta ruwaito cewa a watan Oktoba, 2025, dan Majalisar na Bauchi ya sanar a hukumance cewa ya bar PDP zuwa APC a zauren majalisar dattawa.

A cikin wasiƙar, Sanata Kaila ya danganta matakin da ya dauka da abin da ya bayyana a matsayin "rikicin cikin gida da aka daɗe ba a warware shi ba" wanda ya raunana tsarin jam'iyyar PDP a Bauchi da kasa baki daya.

10. Sanata Jarigbe Agom-Jarigbe

Sanata mai wakiltar Kuros Riba ta Arewa, Sanata Jarigbe Agom-Jarigbe, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2025.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa Jibrin Barau ne ya karanta wasikar sauya shekar Agom-Jarigbe.

Kara karanta wannan

PDP ta manta da adawa, ta koma neman taimako wajen Shugaba Tinubu

Kamar dai yadda aka saba ji, Sanata Jarigbe ya ce rigimar cikin gida ce ta kore shi daga PDP, kuma ya koma APC ne domin ba da gudummuwa wajen ci gaban kasa, cewar Guardian.

11. Sanata Kawu Sumaila

A ranar 7 ga watan Mayu, 2025, Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kudancin Kano ya sauya sheka daga Jam'iyyar NNPP zuwa Jam'iyyar APC, kamar yadda Punch ta kawo.

Kawu Sumaila, shugaban Kwamitin kula da Harkokin Man Fetur, ya sanar da sauya shekarsa a cikin wata wasika da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisa.

A cikin wasiƙar, ya bayyana cewa ficewarsa daga NNPP ta samo asali ne daga rikicin shugabanci a jam'iyyar wanda ya haifar da shari'o'i da rabuwar kai a cikinta.

Sanata Kawu Sumaila.
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdulrahman Kawu Sumaila Hoto: Kawu Sumaila
Source: Twitter

12. Sanata Benson Konbowei

Majalisar Dattawa ta sanar da sauya shekar Sanata Benson Konbowei, mai wakiltar mazabar Bayelsa ta Tsakiya, daga jam'iyyar PDP zuwa APC a watan Oktoba, 2025.

An bayyana hakan a zaman majalisar, awanni 24 kacal bayan da gwamnan jihar, Douye Diri, ya fita daga jam'iyyar PDP, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro

A lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa ke karanta wasiƙar Sanata Konbowei ta sauya sheka, an ruwaito cewa takwaransa na Bayelsa ta Yamma, Sanata Seriake Dickson, ya fice daga majalisar.

13. Sanata Benson Agadagba

Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas, Benson Agadagba, ya sauya sheka zuwa APC daga PDP a watan Oktoba, 2025.

Wannan ya zo ne 'yan kwanaki bayan Sanata Konbowei Benson (Bayelsa ta Tsakiya), ya sauya sheka zuwa APC daga babbar jam'iyyar adawa, cewar Tribune Nigeria.

14. Sanata Ahmed Wadada

A ranar 3 ga watan Satumba, 2025, Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawa, Ahmed Wadada, ya bar SDP zuwa jam'iyyar All APC a hukumance.

NAN ta ruwaito cewa Wadada ya kasance memba na APC kafin ya shiga SDP don tsayawa takarar kujerar Sanata ta Yamma a Nasarawa a shekarar 2023, wanda ya samu nasara.

15. Sanata Kelvin Chukwu

Sanatan da ke wakiltar Gabashin Enugu, Kelvin Chukwu, ya fice daga jam'iyyar LP zuwa APC a ranar Laraba, 8 ga watan Oktoba, 2025.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasiƙarsa ta sauya sheka a zaman majalisa.

Kara karanta wannan

A karon farko cikin shekaru 14, an zabi Najeriya a majalisar IMO ta duniya

Sanata Kelvin Chikwu.
Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Enugu ta Gabas, Sanata Kelvin Chikwu Hoto: Kelvin Chikwu
Source: Facebook

Sanatan, a cikin wasiƙar, ya ce sauya shekarsa ta biyo bayan tattaunawa mai zurfi da ya yi da mutanen mazabarsa da sauran masu ruwa da tsaki.

Majalisar Dattawa ta tabo shirin Safe School

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta soma cikakken bincike kan yadda shirin tsaron makataranty na Safe School ya lalace duk da an narka masa $30m da kuma N144bn.

Wannan ya zo ne yayin zaman farko na kwamitin wucin gadi da Sanata Orji Uzor Kalu daga Abia ta Arewa ke jagoranta don bincike kan yadda aka batar da $30m da rashin tasirin shirin.

Kwamitin ya gayyaci Ministan kudi, Wale Edun, ministan ilimi, Tunji Alausa, da Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, domin yin bayani kan yadda aka kasshe kudaden.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262