Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisun Tarayya Na 10, Muƙamai, Da Jihohin Da Suka Fito

Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisun Tarayya Na 10, Muƙamai, Da Jihohin Da Suka Fito

A ranar Talata, 13 ga watan Yuni ne shugaban ƙasa kuma babban kwamandan askarawan Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da majalisun kasa na 10.

Wannan lokaci ne mai ɗumbin tarihi, wanda ke nuna ƙarfin dimokuradiyyar Najeriya.

'Yan majalisun guda biyu sun zaɓi shugabannin da za su jagoranci tagwayen majalisun na 10.

Cikakken bayani kan shugabannin majalisun Tarayya
Bayanai kan sabbin shugabannin majalisun Tarayya da aka zaba a ranar Talata. Hoto: PM News
Asali: UGC

Sanatoci a Majalisar Dattawa sun zaɓi Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban Majalisar ta 10, wanda ya samu ƙuri’u 63 inda ya doke abokin hamayyarsa Abdulaziz Yari da ya samu ƙuri’u 46.

Haka zalika Barau Jibrin ya zama mataimakin shugaban Majalisar Dattawan ba tare da wata hamayya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ne ya lashe kujerar kakakin majalisar ta 10 da kuri'u 353, yayin da Benjamin Okezie Kalu, ya zama mataimakinsa ba tare da hamayya ba.

Kara karanta wannan

Akpabio Ya Nemi Muhimman Bukatu Guda 2 Wurin Tinubu Bayan Zama Shugaban Majalisar Dattawa Na 10

Bayanan Shugabanin tagwayen Majalisun na 10

A cikin wannan maƙala, Legit.ng ta tattaro muku cikakkun bayanai kan mutanen da za su jagoranci tagwayen majalissun Najeriya, wato na Majalisar Dattawa, da ta wakilai.

1. Godswill Akpabio (Shugaban Majalisar Dattawa)

An haifi Godswill Akpabio, tsohon ministan Neja Delta, a ranar 9 ga Disamba, 1962.

Akpabio ya kammala karatunsa na firamare a makarantar Methodist Primary School, Ukana, sannan ya wuce Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Fatakwal jihar Ribas, inda ya samu takardar shaidar karatu matakin O da na A.

Sanatan ya karanci fannin shari'a a jami'ar Kalaba, kuma ya halarci makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya da ke Legas.

Bayan kammala karatu, ya yi aiki a matsayin malami kuma daga baya ya yi aiki a Paul Usoro and Co, wata ma'aikata mai zaman kanta ta lauyoyi.

Akpabio ya kuma yi aiki da kamfanin sadarwa na EMIS Telecoms Limited, inda ya kai matakin zama Manajan Darakta na kamfanin.

Kara karanta wannan

Abubuwa 11 da Suka Taimaki Tajudden Abbas Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai

A shekara ta 2002, an naɗa shi kwamishinan man fetur da albarkatun ƙasa a jiharsa wato Akwa Ibom. Bayan nan, ya zama gwamnan jihar Akwa Ibom a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a shekarar 2007, sannan an kuma zabarsa a karo na biyu a shekarar 2011.

Akpabio ya zama shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP a shekarar 2013.

A shekarar 2015, ya lashe kujerar Sanata na shiyyar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

Duk a 2015, Akpabio ya zama shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa. A watan Agustan 2018, Akpabio ya yi murabus a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, sannan ya fice daga PDP ya koma jam’iyyar APC.

A watan Yulin 2019, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba da sunan Akpabio a matsayin ministan harkokin Neja Delta. Majalisar dattawa ta tabbatar da shi a watan Agusta na 2019.

A ranar Talata, 13 ga watan Yuni 2023, aka zaɓi Akpabio a matsayin sabon shugaban Majalisar Dattawa bayan ya doke babban abokin hamayyarsa da ƙuri’u 17.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sa Labule da Sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnoni 2 da Ganduje, Bayanai Sun Fito

2. Barau Jibrin (mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa)

Barau Jibrin ɗan asalin garin Kabo ne da ke ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano, kuma an haife shi a shekara ta 1959.

Sanatan ya yi digirinsa na farko a fannin lissafin kuɗaɗe, sannan digiri na biyu a fannin hada-hadar kudi da farashi, ya ƙara wani digirin na biyu a ɓangaren gudanarwa, sannan ya ƙara wani a ɓangaren kula da kasuwanci.

Har ila yau, Barau ya ƙara yin wani digiri na biyu a fannin gudanar da kuɗi akan shawarar kasuwanci daga Jami'ar Cornell, da ke Amurka.

Sanatan ya yi aiki na ɗan takaitaccen lokaci a sashin lissafin kudi na jihar Kano, kafin daga bisani ya yi murabus a shekarar 1992 ya fara sana’arsa mai zaman kanta, wacce ta shafi masana’antu, inshora da gine-gine.

Barau ya fara tsayawa takara ne a shekarar 1999, na kujerar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Tarauni ta jihar Kano kuma ya samu nasara.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da Ya Kamata ku sani Game da Akpabio, Sabon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

A majalisar wakilai, ya taba zama shugaba, kwamitin kasafin kudi na majalisar da kuma mamba a kwamitin samar da wutar lantarki na majalisar a wancan lokacin.

Bayan wa’adinsa ya ƙare a Majalisar Wakilai, Barau ya riƙe muƙamin shugaban hukumar zuba jari da kaddarori ta jihar Kano, sannan ya kuma riƙe muƙamin Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar Kano.

A shekarar 2001, ya kasance mamba a kwamitin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa domin duba tsarin kasafin Kuɗin Najeriya.

A shekarar 2009, Barau ya zama mamba a kwamitin karfafa kasuwanci na jihar Kano.

Daga nan sai Barau ya dawo fagen siyasa, inda ya tsaya takara a shekarar 2015 sannan kuma ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC.

Barau ya zama mataimakin shugaban kwamitin albarkatun man fetur (Downstream), kuma daga baya ya zama shugaban wannan kwamiti.

A ƙarshen shekarar 2016, Barau ya koma kwamitin Majalisar Dattawa kan manyan makarantu na ƙasa (TETfund), a matsayin shugaban kwamitin.

Kara karanta wannan

Bayan Doke Yari, Sanata Akpabio Ya Karɓi Rantsuwa, Ya Kama Aiki Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

Sanatan ya kuma kasance mamba a kwamitin Neja-Delta, masana'antu, sufuri, daidaita kasafin kuɗi da kuma sakataren kungiyar Sanatocin Arewa.

A ranar 3 ga watan Oktoba, 2019, Sanata Barau ya gabatar da ƙudirin kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya ta Kabo.

A watan Oktoban 2022, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa fitaccen Sanatan lambar girmamawa ta ƙasa wato CON.

3. Tajudeen Abbas (Kakakin Majalisar Wakilai)

An haifi Honarabul Tajudeen Abbas a watan Oktoba 1963 a garin Zaria dake jihar Kaduna.

Dan majalisar dai ƙwararre ne a fannin ilimi kuma ɗan siyasa wanda yake wakiltar mazabar tarayya ta jihar Kaduna a Arewacin Najeriya.

Ya halarci Kwalejin Malamai ta Kaduna (KTC), inda ya samu takardar shaidar koyarwa mataki na 2 a shekarar 1981.

Daga nan sai ya wuce zuwa jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya karanci harkokin kasuwanci, wanda ya kammala a shekarar 1988.

Daga nan ya koma domin yin digiri na biyu a fannin kasuwanci a jami'ar a shekarar 1993. Daga nan Abbas ya samu digiri na uku a fannin harkokin kasuwanci a Jami'ar Usman Dan-Fodio da ke Sakkwato a shekarar 2010.

Kara karanta wannan

Godswill Akpabio Ya Doke Abdulaziz Yari, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Ya fara aiki a matsayin malamin firamare daga shekarar 1981 zuwa 1988, kafin daga bisani ya zama malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kaduna a shekarar 1989.

A shekarar 1993 ya koma jami’ar jihar Kaduna (KASU), a matsayin malami zuwa 2001. Daga shekarar 2001 zuwa 2005, Dakta Tajudeen Abbas ya yi aiki a matsayin manajan kasuwanci na NTC Plc.

A shekarar 2011, Abbas ya shiga harkokin siyasa inda ya samu nasarar zama ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Zariya ta jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC.

Ya sake komawa majalisar daga 2015 zuwa 2019, sannan kuma zuwa 2023.

Tajudeen Abbas ya kasance mataimakin shugaban kwamitin bin doka da oda, kuma ya jagoranci kwamitoci da dama da suka haɗa da kwamitin tsare-tsare na bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa, Tsaro, Ayyukan Jama'a da sauransu.

An zabi Tajuddeen Abbas, matsayin kakakin Majalisar Wakilai ta kasa, a ranar Talata, 13 ga watan Yunin 2023.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalilai 5 Da Ka Iya Sa Akpabio Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa

4. Benjamin Kalu (Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai)4. Benjamin Kalu (Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai)

Benjamin Kalu shi ne dan majalisa da ke wakiltar mazaɓar Bende ta jihar Abia, kuma shi ne mai magana da yawun Majalisar Wakilai, sannan kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yaɗa labarai da hulda da jama'a.

An haife shi a ranar 5 ga Mayu, 1971, sannan ya yi digirinsa a Jami'ar Calabar, inda a can ma sai da ya riƙe muƙamin wakilin dalibai. Ya kuma taba zama shugaban 'yan jam'iyyar PDP da ke a ƙasashen waje.

Benjamin Kalu ya riƙe shugabancin ƙaramar hukumar Bende ta jihar Abia yana da shekaru talatin da daya (31).

Bayan nan ya zama babban mai ba gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu shawara na musamman kan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, kafin ya zama babban mai bai wa gwamna shawara kan muradun ƙarni da hulɗar ƙasa da ƙasa.

A shekara ta 2002, Kalu ya tsaya takarar kujerar Majalisar Wakilai amma ya sha kaye a hannun Mbah Ajah.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamnan APC Ya Faɗi Sanatan da Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

A 2011 da 2015, ya ƙara tsayawa takarar ta Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar PPA, inda nan ma ya sha kaye.

A ranar 23 ga watan Fabrairun 2019, Kalu ya samu nasarar lashe zaɓen kujerar, a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki a yayin da ya doke Chima Anyaso na jam’iyyar PDP a mazabar Bende ta jihar Abia.

Sanata Akpabio ya karbi rantsuwar fara aiki bayan kayar da Yari

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa kim kaɗan bayan sanar da nasarar lashe zaɓen shugabancin Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya karɓi rantsuwar fara aiki.

An rantsar da Sanata Akpabio ne a matsayin shugaban Majalisar Dattawan bayan doke abokin karawarsa, Abdulaziz Yari da tazarar ƙuri'u 17.

Asali: Legit.ng

Online view pixel