Malam El-Rufai Ya Faɗi Ministoci da Hadiman da Ya Kamata Tinubu Ya Kora Daga Aiki

Malam El-Rufai Ya Faɗi Ministoci da Hadiman da Ya Kamata Tinubu Ya Kora Daga Aiki

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu kada ya ji kunyar korar duk ministan da ya gaza komai
  • El-Rufai ya ce dukkan ministoci ko hadiman da shugaban ƙasa ya naɗa, idan suka gaza kai matakin da ake tsammani, ya sallame su daga aiki
  • Ya yi wannan furucin ne yayin hira da manema labarai a Maiduguri, ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Malam Nasir El-Rufa'i, tsohon gwamnan jihar Kaduna ya roƙi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ka da ya yi wata-wata, ya kori duk ministan da ya gaza aikin da aka ɗora masa.

Nasir El-Rufa'i ya buƙaci shugaban ƙasar kar ya kuskura ya yi jinkirin korar dukkan ministoci ko hadiman gwamnati da ya naɗa amma suka gaza sauke nauyin da ke kansu.

Kara karanta wannan

Malam El-Rufa'i ya bayyana sunan gwamnan da ya fi sauran gwamnoni aiki a Najeriya

Malam Nasiru.
Tsohon gwamna El-Rufai ya bai wa Bola Ahmed Tinubu shawara Hoto: Mohammaed Bello El-Rufai
Asali: Twitter

Saƙon El-Rufai ga shugaba Tinubu

Tsohon gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da yake kira ga shugaban kasar da ya duba yiwuwar gyara wasu tsare-tsare da ba su dace ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam El-Rufai ya aike da sakon ga shugaban kasar yayin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu.

"Ka nada mutum a muƙami, kuma ba ya ayyuka kamar yadda ake tsammani. Ya kamata a ce kana da ƙarfin zuciyar da za ka sanar da shi cewa kana bukatar gogagge, ya tafi ya kama wani aikin daban."

- Nasir El-Rufai.

Daga nan sai El-Rufai ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi wa shugaba Tinubu addu’a don samun nasara a yunkurinsa na inganta tattalin arzikin kasar nan.

Gwamnati ta dawo da tallafin fetur?

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Malam El-Rufa'i ya bayyana babbar matsala 1 tak da ta addabi Najeriya

Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa har yanzun gwamnatin tarayya na biyan tallafin man fetur, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce mafi yawan ƴan Najeriya ba su san cewa tallafin man fetur ya dawo ba kuma gwamnati tana biyan maƙudan kuɗin da suka zarce na baya.

NNPP ta nemi Yusuf ya sauka

A wani rahoton kuma Wasu mambobin jam'iyyar NNPP a jihohin Arewa 19 sun bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi murabus.

Tawagar masu ruwa da tsakin NNPP karkashin jagorancin Attahiru Musa da sakatare, Simeon Pam, sun kaɗa kuri'ar rashin amincewa da gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel