Gwamna Ya Gamu da Matsala, 'Yan Majalisarsa Sun Nuna Masa Karfin Ikonsu a Doka

Gwamna Ya Gamu da Matsala, 'Yan Majalisarsa Sun Nuna Masa Karfin Ikonsu a Doka

  • Majalisar dokokin Ribas ta bijirewa gwamnan jihar Siminalayi Fubara ta amincewa da kudirin kananan hukumomi ya zama doka
  • A ranar 13 ga watan Maris ne majalisar ta mika wa Fubara kudurin domin amincewa amma gwamnan ya ki rattaba hannu a kai
  • Amma a yau Litinin kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar suka kada kuri’ar bijirewa gwamnan tare da sannu kudurin ya zama doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Ribas - Majalisar dokokin jihar Ribas ta amince da kudurin gyara dokar kananan hukumomin ya zama doka ba tare da amincewar gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ba.

Majalisar a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu, ta bijirewa umarnin babbar kotun jihar da ta dakatar da ita daga gyara dokar tsawaita wa’adin shugabannin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Hukumar JAMB ta dauki mataki kan wasu jami'anta da suka ci zarafin daliba mai hijabi

Majalisar jihar Ribas ta rattaba hannu sabuwar doka ba tare da izinin Fubara ba
Kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar ne suka kada kuri’ar rattaba hannu kan dokar. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Facebook

Majalisar dokoki ta bijirewa Gwamna Fubara

A cewar majalisar, kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar sun kada kuri’ar bijirewa gwamnan tare da amincewa da kudirin ya zama doka, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba a ranar 13 ga watan Maris ne majalisar ta zartar da dokar kananan hukumomi sannan ta mika wa Fubara don amincewa amma gwamnan ya ki amincewa da kudirin.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa majalisar ta kuma tantance tare da tabbatar da shugaba da sauran mambobin hukumar kula da majalisar bisa wannan sabuwar doka.

Wadanda aka tantance kuma aka tabbatar su ne Sampson Worlu a matsayin shugaba tare da Abinye Pepple, Blessing Derefaka, Gbaranen Robinson da Dorcas Amos a matsayin mambobi.

Majalisar Ribas ta ba kanta karfin iko

A ranar 22 ga Maris, 2024, majalisar jihar ta zartar da dokar Majalisar Dokokin Jihar Ribas (wadda ta sabunta) a matsayin doka.

Kara karanta wannan

Kwara: Gwamnati ta fara bincike kan zargin ana sayar da naman shanu mai guba

Da wannan dokar, yanzu majalisar ta ba wa kanta ikon nada shugaba da mambobin hukumar kula da ayyuka na majalisar jihar.

Mambobin majalisar 27 da ke biyayya ga Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, sun jima suna takun saka da Gwamna Fubara.

'Yan sandan jihohi: Matsayar IPG Egbetokun

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya nuna adawa kan kirkirar 'yan sandan jihohi.

IGP Egbetokun ya yi nuni da cewa gwamnoni na iya amfani da 'yan sandan wajen cimma muradun siyasa wanda zai jawo tauye hakkin dan Adam da rigingimun siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel