Yan Sanda Sun Kwace Iko da Majalisar Dokokin Jihar Ribas Bayan Rikici Ya Tsananta

Yan Sanda Sun Kwace Iko da Majalisar Dokokin Jihar Ribas Bayan Rikici Ya Tsananta

  • Dakarun yan sanda sun mamaye zauren majalisar dokokin jihar Ribas a wani martani bayan rikicin siyasa ya ƙara tsanani
  • Shugabannin majalisar na tsagi biyu sun gudanar da zama a wurare daban-daban ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba
  • Daga cikin abubuwan da suka tattauna, ƴan majalisar sun yi nazari kan yadda za a kawo ƙarshen yajin aikin da ma'aikatan majalisa ke yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Dakarun rundunar ƴan sanda sun kwace iko da zauren majalisar dokokin jihar Ribas biyo bayan ƙaruwar rikicin siyasa.

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa rikicin siyasar da ya ɓalle a majalisar tun kwanakin baya ya ƙara tsananta ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamna, shugaban majalisar dokoki da mataimakinsa sun yi murabus a jihar arewa

Majalisar dokokin jihar Ribas.
Yan Sanda Sun Kwace Iko da Majalisar Dokokin Jihar Ribas Bayan Rikici Ya Tsananta Hoto: Bright Jossy
Asali: Facebook

Punch ta tattaro cewa dakarun ƴan sandan sun girke motocin sintiri cikin jiran ko ta kwana a ƙofar shiga zauren majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa an taƙaita zirga-zirgan ababen hawa a titin Moscow, wanda ke kusa da majalisar dokokin.

Haka nan kuma an ga jami'an tsaron sun mamaye wurare masu muhimmanci a yankin majalisar domin tabbatar da doka da oda.

Me yan majalisar suka tattauna a zaman da suka yi?

Legit Hausa ta gano cewa mambobin majalisar guda 25 ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar, Martin Amaewhule, sun yi zama tun da safiyar ranar Talata.

Rahotanni sun nuna cewa yan majalisar sun tattauna kan batutuwa guda biyu, na farko kan yadda za a kawo karshen yajin aikin da ma'aikatan majalisa ke yi.

Abu na biyu kuma sun yi kira ga kwamishinan ƴan sandan jihar, Olatunji Disu, ya gudanar da bincike kan fashewar da aka samu a majalisar, wanda ya ƙone wani sashi.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Yadda dakarun sojoji suka daƙile harin da 'yan ta'adda suka kai wa ayarin gwamnan APC a arewa

Haka nan kuma a zaman, mambobin majalisar sun yabawa Gwamna Similanayi Fubara bisa ayyukan ci gaban da ya ɗauko da tsarukan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Ribas.

Shugaban Majalisar Dokokin Filato da Mataimakinsa Sun Yi Murabus

A wani labarin kuma Kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Moses Thomas, da mataimakinsa, Gwottaon Fom, sun yi murabus daga muƙamansu.

Jim kaɗan bayan haka mambobin majalisar suka zaɓi sabbin shugabannin da za su maye gurbinsu a majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel