“Najeriya Ba Ta Shirya Ba”: IGP Egbetokun Ya Yi Adawa da Kafa ’Yan Sandan Jihohi

“Najeriya Ba Ta Shirya Ba”: IGP Egbetokun Ya Yi Adawa da Kafa ’Yan Sandan Jihohi

  • A halin yanzu, gwamnatocin jihohi ba su da kudin da za su samar da ‘yan sandan jihohinsu da za su dace da tsarin kasa
  • Wannan ita ce maganar da Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun ya yi a Abuja a ranar Litinin, 22 ga Afrilu
  • IGP Egbetokun ya kuma yi ikirarin cewa wasu gwamnonin za su yi amfani da ‘yan sandan domin biyan bukatun siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya bayyana matsayar rundunar ‘yan sandan Najeriya kan shirin kirkiro da ‘yan sandan jihohi.

A wani taron tattaunawa na yini daya kan lamarin a Abuja a ranar Litinin, 22 ga Afrilu, IGP Egbetokun ya ce Najeriya ba ta shirya amfani da ‘yan sandan jihohi ba.

Kara karanta wannan

Neman kudi: "Mun kashe Bafullatana domin yin tsafi", malamin tsibbu ya fallasa abokansa

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi adawa da samar da 'yan sandan jihohi
IGP Egbetokun na da ra’ayin cewa samar da ‘yan sandan jiha zai kawo illa fiye da alfanunsa. Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

"Illar kirkirar ‘yan sandan jihohi" - IGP Egbetokun

Sufetan 'yan sandan ya bayyana cewa kirkirar ‘yan sandan jihohi zai haifar da rikicin kabilanci, wanda zai kai ga rashin jituwa a jihohin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta rahoto AIG Ben Okolo wanda ya wakilce Egbetokun ya ce kafa ‘yan sandan jihohi zai kuma kai ga kafa wasu rundunoni da dama a fadin Najeriya.

Jami'in ya yi nuni da cewa akwai yiyuwar gwamnonin jihohi suyi amfani da ‘yan sandan a wajen cimma wata manufa ta siyasa, lamarin da zai haifar da take hakkin dan Adam.

Taron dai ya samu halartar manyan 'yan siyar Najeriya da suka hada da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Goodluck Jonathan da Abdulsalami Abubakar, rahoton Channels TV.

"A inganta aikin ‘yan sanda" - IGP Egbetokun

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da ake zargi da hannu rikicin da ya barke a kasuwar Sokoto

IGP Egbetokun ya yi imanin cewa gwamnatocin jihohi ba su da isassun kudin da ake bukata na iya daukar nauyin aikin ‘yan sandan da Najeriya ke bukata.

A madadin hakan, ya ba da shawarar hadewar hukumar tsaro ta NSCDC da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) domin kafa sashe daya a rundunar.

Ya kuma ce akwai bukatar daukar ‘yan sandan da bai gaza 30,000 ba a duk shekara domin cimma muradun Majalisar Dinkin Duniya na aikin ‘yan sanda na zamani.

Mataimakin kwamishina ya halaka kansa

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Gbolahan Oyedemi ya halaka kansa ta hanyar rataya.

Wannan mummunan lamari ya faru ne a garin Ogbomoso, jihar Oyo a yayin da ya je hutun bikin Easter da aka gudanar a makonnin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel