An Shiga Yamutsi a Jihar da APC ke Mulki, Shugabanni 2 Sun Fito a Zaben Majalisa

An Shiga Yamutsi a Jihar da APC ke Mulki, Shugabanni 2 Sun Fito a Zaben Majalisa

  • Shugabanni biyu aka samu a sabuwar majalisar dokokin jihar Nasarawa a dalilin sabanin siyasa
  • A makon nan aka rantsar da ‘yan majalisa a jihohi, zabuka dabam-dabam aka shirya a Nasarawa
  • ‘Yan bangaren Daniel Ogazi sun yi zabensu a majalisa, wasu sun ware sun zabi Balarabe-Abdullahi

Nasarawa - Rikicin da ake fama da shi a majalisar dokokin jihar Nasarawa ya jawo an samu shugabanni biyu da suke ikirarin su aka zaba.

Kamar yadda rahoto ya zo daga Daily Trust, Ibrahim Balarabe-Abdullahi da Daniel Ogah Ogazi su na da’awar shugabancin majalisar ta Nasarawa.

Balarabe Abdullahi shi ne tsohon shugaban majalisa mai wakiltar mazabar Kokana ta gabas, ya shafe shekaru takwas ya na rike da kujerar.

A gefe guda kuma akwai Daniel Ogah Ogazi wanda wannan karo yake cewa ya zama sabon shugaban majalisa, ya gaji Ibrahim Balarabe-Abdullahi.

Kara karanta wannan

Zabe Saura Kwana 5, Shugaban kasa Ya Gagara Shawo Kan Zababbun ‘Yan Majalisa

Majalisa
Abdullahi Sule a Majalisa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Guardian ta ce an zabi Balarabe-Abdullahi ne a wani zama da aka yi a ma’aikatar kananan hukumomi da harkar masarautu a garin Lafiya.

A wannan zabe da aka yi a ma’aikatar gwamnati a maimakon majalisa, Hon. Jecob Kudu mai wakiltar Nasarawa Eggon ne ya zama mataimaki.

Hon. Muhammed Adamu Omadefu Keana ya tsaida shugaban majalisar wannan bangare, a nan take ya samu goyon bayan Hon. Danladi Jatau.

Ogazi ya hada-kai da PDP

Shi kuwa Rt. Daniel Ogah Ogazi ya lashe zabe ne bayan abokan aikinsa 13 sun yi zama, sun zabe shi a zauren majalisar dokoki cikin dar-dar.

Kilakin rikon kwarya a majalisar Nasarawa, Ibrahim Musa ya rantsar da Rt. Hon. Balarabe-Abdullahi wanda ya samu kuri'a 11 a matsayin shugaba.

A yanzu haka ana ta kaddamar da majalisun dokoki a jihohin kasar. ‘Yan majalisar ne ke da hakkin yin dokoki da kuma sa wa masu mulki ido.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Wasu ‘Yan G7 Sun Ki Zuwa Taron da Bola Tinubu Ya Kira

Kundin tsarin mulki ya ba ‘yan majalisa gashin kan su a Najeriya. Majalisa bangare ce mai zaman kan ta kamar masu zartarwa da masu shari’a.

Zaben jihar Osun

A Osun, rahoton da aka samu a makon nan shi ne zababbun ‘yan majalisa sun zabi mai kasa da shekaru 40 ya zama Shugabansu a wannan karo.

Rt. Hon. Adewale Egbedun zai jagoranci majalisar dokokin tare da Akinyode Oyewusi. A shekarar 1985 aka haifi Egbedun, ya yi karatu ne a Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel