Kakakin Majalisar Dokoki Ya Aike da Saƙo Na Musamman Kan nasarar Gwamnan Arewa a Kotun Ƙoli

Kakakin Majalisar Dokoki Ya Aike da Saƙo Na Musamman Kan nasarar Gwamnan Arewa a Kotun Ƙoli

  • Shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa ya aike da saƙo ga yan adawa bayan karkare shari'ar zaben Nasarawa a kotun ƙoli
  • Honorabul Ɗanladi Jatau ya buƙaci yan adawa su haɗa hannu da gwamnatin Abdullahi Sule domin kyautata rayuwar al'umma
  • A cewarsa, shari'a ta kare tunda kotun koli ta tabbatar da Gwamna Sule a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓe a watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Danladi Jatau, ya buƙaci abokan hamayyar Gwamna Abdullahi Sule a zaben gwamnan da ya gabata da su marawa gwamnatinsa baya.

Ya yi wannan roko ga ƴan adawa ne a lokacin da yake hira da manema labarai kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, ranar Litinin a Lafiya, Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan

An Kama Shugaban Ƙaramar hukuma da wani bisa hannu a yunkurin kashe kakakin majalisa a Arewa

Takaddamar jihar Nasarawa.
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Aike da Sako Ga Yan Adawa Bayan Hukuncin Kotun Koli Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Twitter

Kakakin majalisar ya ƙara da cewa mulki na Allah ne kuma yana bada shi ga wanda ya so, kuma ya bai wa Gwamna Sule damar jagorancin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya aike da saƙo ga yan adawa a Nasarawa

Jatau ya roƙi dukkan yan adawa su rungumi hukuncin da kotun ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar Abdullahi Sule na APC a zaben 18 ga watan Maris.

A kalamansa, Danladi Jatau ya ce:

"Hukuncin Kotun Ƙoli ya ƙara tabbatar da zaɓin da al'umma suka yi wa Gwamna Sule ranar 18 ga watan Maris, 2023. Ina kira ga ƴan hamayya da mazauna jihar su karɓi nasarar Sule da imani domin mulki na Allah ne.
"Zaɓe ya zo kuma ya wuce, takaddamar shari'ar ta zo ita ma ta wuce, yanzu lokaci ne na shugabanci, mu haɗu mu marawa gwamna baya a kokarinsa na gina jihar mu da inganta rayuwar al'umma."

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya nuna gwamnan arewa 1, ya bayyana ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

Ya kamata mutane su guji siyasar ƙabilanci

Shugaban majalisar ya bukaci al’ummar jihar da su guji siyasar kabilanci da addini domin zaman lafiya, hadin kai da samun ci gaba mai ɗorewa.

Ya kuma ba da tabbacin cewa majalisar dokokin Nasarawa ta 7 karkashin jagorancinsa zata ci gaba da yauƙaƙa alaƙa da ɓangaren zartarwan gwamnati.

Ya ce kawo yanzu gwamnan ya nuna himma da kishin ci gaban jihar duba da adadi da ingancin ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar kawo yanzu.

An sanar da ranar jana'izar tsohon gwamnan Ondo

A wani rahoton kuma Iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo sun fitar da sanarwa kan shirye-shiryen jana'izar Rotimi Akeredolu.

Bayan kammala duk wasu tarukan addu'o'i da bankwana, za a yi wa Akeredolu jana'iza a binne shi ranar 23 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel