Bai Kamata a Fara Sukar Gwamnatin Tinubu Ba Daga Yanzu, Shehu Sani Ya Bayyana Dalili

Bai Kamata a Fara Sukar Gwamnatin Tinubu Ba Daga Yanzu, Shehu Sani Ya Bayyana Dalili

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana lokacin da yafi dacewa a soki gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC
  • Tsohon dan majalisar ya ce sojoji da ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro na samun ci gaba sosai a gwamnatin Tinubu
  • Sani ya ce dole ne shugaba Tinubu ya tashi ya yi abin da ake bukata domin ba shi da lokacin batawa a halin da ake ciki

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar KadunaTsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce an samu ci gaba ta fuskar tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna tun bayan hawan shugaban kasa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ina sukar biyan da kudin fansa a baya, sai da aka sace ni na gane, tsohon shugaban DSS ya magantu

Sani ya ce har yanzu ana ci gaba da yin garkuwa da mutane a wannan yanki, amma an samu raguwar aukuwar hakan idan aka kwatanta da halin da mutane suka shiga a gwamnatin Muhammadu Buhari.

Bai kamata a fara sukar gwamnatin Tinubu ba, Shehu Sani
A yanzu ya kamata a fara sukar gwamnatin Tinubu ba, Shehu Sani | Hoto: Shehu Sani/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar shafin Twitter da ya yi da Legit mai taken "Tackling Corruption or Insecurity: Priorities for the FG in 2024" a ranar Laraba 31 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane yanayi ake ciki a Najeriya?

Da yake jawabi, Sani ya ce:

“Har yanzu ana ci gaba da yin garkuwa da mutane, ana kuma yin garkuwa da mutane sannan kuma ‘yan ta’adda na ci gaba da tada zaune tsaye. Amma zan iya ce muku kwatankwacin abin da sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ke yi a yau ya fi inda muka fito.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya bayyana hanya 1 da za a bi domin magance cin hanci da rashawa Najeriya

“A baya kusan ba zai yiwu mutane su tashi daga Kaduna zuwa Abuja ba. Amma yanzu abubuwan da ake gani ragu ainun."

Tsohon dan majalisar ya ce a baya ya zama dole mutane su siyar da kadarorin su ko kuma su ci bashi mai yawa don biyan kudin fansa kan sace ‘yan uwansu.

Ya kamata a fara sukar Tinubu?

Da yake magana game da masu sukar gwamnatin Tinubu, shugaban ya ce akwai sauran lokaci idan ma za a soki mulkin Bola Tinubu.

A cewarsa:

“Na yi imanin cewa watanni shida/bakwai sun yi wuri amma bai kamata mu sakankance ba duba da gwamnatin da ta gabata. Abu mafi kyau shi ne yanzu dai a ba su lokaci don ganin abin da za su iya cimmawa. "

Ya kara da cewa:

"Shugaban kasa ba shi da wani lokacin da batawa, dole ya farka ya yi abin da ya kamata, shi ya sa aka zabe shi."

Kara karanta wannan

Bayan shafe kusan mako a hannun 'yan bindiga, dalibai da malaman makaranta sun shaki iskar 'yanci

An nemi Tinubu ya tsige ministocinsa

A wani labarin, kungiyar masu fasahar kirkirar shafukan yanar gizo (Bloggers and Vloggers, Content Creators Association in Nigeria) ta aike da sako ga Bola Tinubu.

Kungiyar wadda ake kira da BAVCCA a takaice ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya raba gari da dukkan ministocin da suka gaza aikin da aka dora musu.

A rahoton Leadership, ta kara da cewa ya zama wajibi shugaban kasa ya kare martabar gwamnatinsa ta hanyar kin sassauta wa ragwagen ministoci da marasa gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel