Yadda El-Rufai Ya Nemi a Soke Kotun Shari’a da Gargajiya Inji Tsohon Shugaban Majalisa

Yadda El-Rufai Ya Nemi a Soke Kotun Shari’a da Gargajiya Inji Tsohon Shugaban Majalisa

  • Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, ya hana a rusa kotun shari’a da kotun gargajiya
  • Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani ya yi ikirarin Nasir El-Rufai ya aiko da kudiri a rusa kotunan a doka
  • Amma wasu abokan aikinsa sun shaida cewa gwamnatin baya ba taba shigo da wannan kudiri ba

Kaduna - A wani faifai da ya rika yawo tun makon jiya, an ji Tanimu Yusuf Zailani ya na magana a kan wa’adinsa a matsayin shugaban majalisa a Kaduna.

A wannan faifai da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi a Twitter, an ji Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani ya yi bayanin halin tsaka mai wuya da ya shiga a majalisa.

Tsohon shugaban majalisar dokokin ya ce tsohon Gwamna, Nasir El-Rufai ya kawo masu kudirin soke kotunan shari’a da kotun gargajiya daga jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Tinubu: Malamin Addini Ya Gargadi Shugaban Kasa Game Da Ba Wa El-Rufai Mukami, Ya Fadi Dalilansa

Shugaban Majalisar Kaduna
Tsohon Shugaban Majalisar Kaduna, Hoto: SpeakerZailani
Asali: Twitter

A cewar Yusuf Zailani, da a ce majalisar Kaduna ta yi na’am da wannan kudiri ya zama doka, Allah kadai ya san irin halin da jihar za ta tsinci kan ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An fatattaki kudirin Gwamnati

A zaman karshe da majalisar da ya jagoranta tayi, an ji Zailani ya nemi hadin-kan abokan aikinsa domin ayi fatali da wannan kudiri, kuma hakan aka yi.

Kamar yadda ‘dan majalisar mai wakiltar Igabi ta yamma ya fada, kudirin soke wadannan kotu ne silar duk halin ha’ula’i da ya samu kan shi a siyasa.

Zailani yake cewa ko da kudirin nan da aka turo a ranar 30 ga watan Junairun 2023 kadai ya iya sokewa, ya na alfahari da shekarun da ya yi a kan kujera.

Kafin karkare zaman aka samu Honarabul Emmanuel Bako Kantiok ya mike ya bukaci ayi fatali da kudirin, Kantioka yana wakiltar mazabar Zonkwa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Umarci Shettima Ya Fito da Tsarin Taimakon Talaka Bayan Janye Tallafin Fetur

Legit.ng Hausa ta fahimci wannan yunkuri ya samu yardar Honarabul Sagir Maigana. A karshe hakan ya bada dama majalisar dokoki ta soke kudirin.

"Karya ne, ba gaskiya ba ne"

Amma rahoto ya zo daga Punch cewa Hon. Yusuf Salihu mai wakiltar mazabar Kawo ya karyata wannan magana, ya ce ba ayi haka a majalisar dokokin ba.

Da yake magana tare da Hon. Shehu Yunusa mai wakiltar Kubau, ‘dan majalisar ya shaidawa manema labarai ba a taba yunkurin soke wadannan kotu ba.

Salihu ya yi kira ga Zailani da ya guji fadin abin da ba gaskiya ba musamman a kan batun shari’a.

Majalisa ta na hannun Iyan Zazzau

Hon. Tajuddeen Abbas wanda ya fara aiki a matsayin malamin makarantar firamare zai rike Majalisa kamar yadda rahoto ya zo cewa ya lashe zabe da aka yi.

Nasir El-Rufai ya na cikin wadanda suka tallata Iyan Zazzau, har ya samu goyon bayan jam’iyyarsa ta APC. Tun 2015 Abbas ya ke wakiltar mazabar Zariya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel