Attahiru Jega Ya Bayyana Abu 1 da Ya Kamata a Bincika Kan Zaben 2023

Attahiru Jega Ya Bayyana Abu 1 da Ya Kamata a Bincika Kan Zaben 2023

  • Farfesa Attahiru Jega ya bayyana ra’ayinsa kan gazawa da rashin aiki na fotal ɗin nuna sakamakon zaɓe (IReV) a lokacin zaɓen 2023
  • Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ya zargi ƴan siyasa cewa suna da hannu a cikin wannan matsala
  • Jega mai shekara 67 a duniya, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin, ya buƙaci a gudanar da bincike kan lamarin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi kira da a gudanar da bincike kan yadda fotal ɗin kallon sakamakon zaɓe na (IReV) ya kasa aiki a lokacin zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya kori wasu hadimai daga aiki a gwamnatinsa, ya naɗa sabbi nan take

Jega ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, 26 ga watan Janairu, a lokacin da yake hira da Laolu Akande a shirin 'Inside Sources' na tashar Channels tv.

Jega ya yi magana kan zaben 2023
Jega ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar sa hannun yan siyasa kan gazawar iRev Hoto: Stringer
Asali: Getty Images

A ranar 25 ga Fabrairu, 2023, hukumar ta fuskanci matsaloli wajen shigar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa cikin gaggawa a fotal ɗin iRev, wanda hakan ya saɓa wa sashi na 60 na dokar zaɓe ta 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jega ya zargi ƴan siyasa kan rashin aikin iREV

Jega ya yi hasashen cewa duk da ƙoƙarin INEC, akwai yiwuwar tsoma baki daga ƴan siyasa waɗanda idonsu ya kulle saboda mulki a cikin tsarin IReV.

A kalamansa:

"Idan ka tambayi ra'ayi na, ina jin cewa INEC na buƙatar ta yi mana ƙarin bayani game da abin da ya faru da IReV.
"A zahiri, a wani lokaci, har ma na yi kira da a yi cikakken game da abin da ya faru da IReV.

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya sassauta dokar zaman gida ta awanni 24 da ya sanya a Mangu, ya faɗi dalili 1

"Ina jin cewa wani abu ya faru, duk da ƙwarin gwiwa da yadda shugaban INEC (Mahmood Yakubu) ya yi magana game da IreV, sai gashi ya gaza.
"Na yi imanin cewa wasu daga cikin gurɓatattun ƴan siyasarmu, ƙila sun yi kutse cikinsa amma laifin INEC ya kamata a gani kan hakan."

Bayan kammala warware shari’o’in kotu, Jega ya jaddada cewa dole ne INEC ta yi bincike sosai kan al’amuran IReV.

Jega Ya Samu Sabon Muƙami

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya naɗa Farfesa Attahiru Jega, sabon muƙami a jiharsa.

Gwamna Sule ya naɗa tsohon shugaban hukumar INEC ɗin ne a matsayin muƙamin uban jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel