Tsohon Shugaban INEC, Jega Ya Soki Hukuncin Zaben Gwamnan Kano, Ya ba Tinubu Shawara

Tsohon Shugaban INEC, Jega Ya Soki Hukuncin Zaben Gwamnan Kano, Ya ba Tinubu Shawara

  • Attahiru Jega ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake amfani da alkalan kotu domin ruguza zaben da INEC ta shirya
  • Tsohon shugaban hukumar zabe na kasa (INEC) ya yi tir da abin da ya faru wajen hukuncin zaben gwamnan jihar Kano
  • Farfesa Jega ya kawo shawarar a sake duba nadin INEC REC tare da magance matsaloli irinsu sayen kuri’un talakawa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Attahiru Jega wanda ya jagoranci hukumar zabe na kasa (INEC) a baya, ya damu da yadda kotu ta ke soke zabe a Najeriya.

Tsohon shugaban na hukumar INEC ya shiga sahun masu sukar irin rawar da alkalai su ke takawa wajen tsaida shugabannin siyasa.

Leadership ta rahoto Farfesa Attahiru Jega ya na cewa akwai bukatar a raba kotuna da shiga harkar siyasa da sunan shari’ar zabe.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Atoni Janar na Kano Dederi ya shiga matsala, an nemi a hukunta shi

Farfesa Attahiru Jega
Attahiru Jega wanda ya rike INEC Hoto: 21stcenturychronicle.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin cin hanci a shari'an zabe

Jega ya kuma nuna muhimmancin a magance batun zargin da ake yi na son kai da karbar cin hanci da rashawa a wajen shari’o’in zabe.

Yayin da jama’a su ke ta korafi a yau, Farfesan ya kawo shawarar a gyara dokar zabe kuma a fito da dokoki da za su kare damukaradiyya.

Shari'ar zaben Gwamnan Kano

A hirar da tashar Channels ta yi da shi, Jega ya yi Allah wadai da kwamacalar da kotun daukaka kara ta tafka a shari’ar gwmanan Kano.

Tsohon shugaban jami’ar ta Bayero ya yi kira da babban murya da binciki yadda hukuncin zaben Kano ya sha bam-bam da bayanan CTC.

Jega yana so Najeriya ta yi koyi da kasar Indiya, inda ake raba harkar zabe da kara a kotu.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro sun cika ko ina, NNPP da APC sun hakura da zanga zanga a Kano

Farfesa Jega yana so a shiryawa zaben 2027

Kyau ayi gaggawan yin kwaskwarima a dokar zaben 2022 ta yadda gyare-gyaren za su fara aiki nan da babban zabe mai zuwa na 2027.

Wata matsala da masanin ya yi magana a kai ita ce amfani da kudi wajen sayen kuri’a, ya ce attajiran siyasa na amfana da talaucin mata.

"Tinubu ya duba nadin INEC REC" - Jega

Bayan haka kuma, Jega ya bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake duba nadin wasu daga cikin Kwamishinonin zabe da ya yi a INEC.

A ra’ayin Farfesan ilmin siyasar, ya kamata majalisar dattawa ta rika bi da kyau wajen tantance wadanda za su zama kwamishinonin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel