Tsohon Shugaban INEC, Jega, Ya Bukaci Kawo Sauyi Kan Nadin Da Shugaban Kasa Ke Yi Na Hukumar

Tsohon Shugaban INEC, Jega, Ya Bukaci Kawo Sauyi Kan Nadin Da Shugaban Kasa Ke Yi Na Hukumar

  • Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar INEC ya bukaci a sauya kundin tsarin mulki na nadin shugaban hukumar
  • Jega ya bayyana haka ne yayin wani babban taro da ya halarta a yau Asabar a jihar Akwa Ibom
  • Ya shawarci sauya dokar nadin shugaban hukumar da shugaban kasa ke yi don kaucewa zargin amshi shatan shugabannin hukumar

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Attahiru Jega ya bukaci a yi gyara a kundin tsarin mulki kan nadin shugaban hukumar.

Jega ya ce bai kamata ace shugaban kasa ba ne ke da ikon nada shugaban hukumar INEC Legit ta tattaro.

Jega ya bukaci sauya kundin tsarin mulki na nadin shugaban INEC
Tsohon shugaban INEC, Jega ya yi martani kan tsarin nadin shugaban INEC. Hoto: Elder Solomon Harry.
Asali: Facebook

Meye Jega ke cewa kan nadin shugaban INEC?

Farfesan ya kara da cewa hakan ne kadai zai rage zargin cewa shugabannin hukumar 'yan amshin shatan shugaban kasa ne.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Amince Da Nadin Sabbin Shugabanni Biyu a Ma’aikatar Lafiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Attahiru ya bayyana haka ne yayin wani babban taro da cibiyar NILDS ta shirya a jihar Akwa Ibom.

Daily Trust ta tattaro Jega na cewa:

"Ya kamata a yi gyara a kundin tsarin mulki musamman wanda ya shafi nadin shugaban hukumar INEC.
"Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar INEC ba, hakan ne zai rage zargi na juya shugabannin hukumar daga mutane."

Wane shawara Jega ya bayar kan nadin shugaban INEC?

Ya kara da cewa:

"Ina ba da shawarar cewa ya kamata kwamitin hadin gwiwa su bincika tare da tabbatar da rashin shiga lamuran siyasa a yayin nadin.
"Ya kamata mutane ma su yi bincike kan kwarewa da kuma dacewa don tabbatar da sahihancinshi da kuma ba da damar tura korafi daga jama'a."

Wannan na zuwa ne yayin da mafi yawan 'yan kasa ke ganin shugabannin hukumar INEC da shugaban kasa ke nadawa ba su isa hana shi mulki ba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Amince Da Nadin Sabon Mai Binciken Kudi Na Kasa

Hukumar INEC na tunani kan tsaro a Imo

A wani labarin, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta na nazari kan rashin tsaron da ke kara ta'azzara a yankin Kudu maso Gabas.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a jihar Imo a watan Nuwamba.

Har ila yau, hukumar za ta gudanar da zabuka a jihohin Kogi da Bayelsa duk a watan Nuwamba mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel