PDP Munafukai Ne, Korarren Dan Majalisa Ya Sha Alwashin Komawa Kujerarsa Ko a Mutu, Ya Fadi Dalili

PDP Munafukai Ne, Korarren Dan Majalisa Ya Sha Alwashin Komawa Kujerarsa Ko a Mutu, Ya Fadi Dalili

  • Ana ci gaba da samun shakku kan hukuncin Kotun Daukaka Kara bayan wani dan Majalisa ya ce sai ya koma kujerarsa
  • Hon. Destiny Nwagwu wanda Kotun ta rusa zabensa ya ce babu abin da zai hana shi komawa kujerarsa
  • Destiny ya ce hukuncin kotun da ya rusa rusa zabensa bai halatta ba inda ya ce da shi za a koma zaman Majalisar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Korarren dan Majalisar jihar Abia, Hon. Destiny Nwagwu ya sha alwashin komawa kujerarsa.

Destiny ya ce hukuncin kotun da ya rusa rusa zabensa bai halatta ba inda ya ce da shi za a koma zaman Majalisar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ashiru, dan takarar PDP ya fadi abin da zai yi nan gaba bayan shan kasa a Kotun Koli

Dan Majalisa ya sha alwashin komawa kujerarsa ko ta halin-kaka
Korarren Dan Majalisa, Destiny Nwagwu Ya Sha Alwashin Komawa Kujerarsa. Hoto: Hon. Destiny Nwagwu.
Asali: Facebook

Yaushe aka rushe zaben dan Majalisar a Abia?

A ranar 30 ga watan Nuwamba, Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben Destiny wanda dan jam'iyyar LP ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta tabbatar da nasarar Hon. Uzodike Aaron a matsayin wanda ya lashe zaben, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Yayin da ya ke ganawa da 'yan jaridu, Nwagwu ya ce har yanzu shi ne zababben dan Majalisar a mazabar Abia ta Arewa.

Wane martani dan Majalisar ya yi kan kujerar?

Nwagwu ya ce ya na mamakin yadda korarrun 'yan Majalisu a Plateau ke kuka yayin da shi kuma a nan an matsa a rantsar da dan jam'iyyar PDP, Hon. Aeron.

Ya ce wannan kuka da PDP ke yi munafurci ne inda ya sha alwashin komawa kujerarsa karfi da yaji, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Bayan sha da kyar a Kotun Koli, Gwamnan Arewa ya roki alkalai su sake zama a shari'ar 'yan Majalisu

Ya ce:

"Rashin Adalci a ko ina rashin adalci ne babu bambanci."

Har ila yau, PDP ta bukaci kakakin Majalisar, Hon. Emmanuel Emeruwa ya yi gaggawar rantsar da Hon. Aeron a kujerarsa.

Korarrun 'yan Majalisu 16 sun sha alwashi

Kun ji cewa 'yan Majalisu 16 da aka rusa zabensu a Plateau sun sha alwashin komawa kujerunsu a zaman Majalisar da aka yi jiya Talata.

Mambobin sun ce akwai rashin adalci ganin yadda Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Mutfwang wanda su ke jam'iyya daya.

Sai dai jami'an 'yan sanda ba su musu ta dadi ba bayan watsa musu barkonon tsohuwa da suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel