Bayan Sha da Kyar a Kotun Koli, Gwamnan Arewa Ya Roki Alkalai Su Sake Zama a Shari’ar ’Yan Majalisu

Bayan Sha da Kyar a Kotun Koli, Gwamnan Arewa Ya Roki Alkalai Su Sake Zama a Shari’ar ’Yan Majalisu

  • Gwamnan jihar Plateau ya bukaci alkalan kotu su sake duba hukuncin Kotun Daukaka Kara a jihar
  • Gwamnan ya na magana ne kan hukuncin kotun da ta rusa zaben dukkan ‘yan Majalisun jihar da na Tarayya
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya sha da kyar a Kotun Koli da ta tabbatar da shi a matsayin gwamna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau – Gwamna Caleb Muftwang ya bukaci a sake zama don duba hukuncin Kotun Daukaka Kara.

Caleb ya ce hukuncin da kotun ta yanke kan ‘yan Majalisun Tarayya da na jihohi babu adalci a ciki, cewar Premium Times.

Gwamnan Arewa ya bukaci a sake zama kan hukuncin Kotun Daukaka Kara
Gwamna Caleb Ya Roki Alkalai Su Sake Zama a Shari’ar ’Yan Majalisu. Hoto: Caleb Muftwang.
Asali: Facebook

Mene Caleb ke cewa kan hukuncin kotun?

Kara karanta wannan

El-Rufai ne silar daukaka ta, Abbas ya fadi karin mutum 1 da ba zai manta da shi ba

Idan ba a mantaba, Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben dukkan ‘yan Majalisun jihar da na Tarayya kan rashin tsarin jam’iyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma abin mamaki kuma Kotun Koli ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar wanda shi ma ya na karkashin jam’iyyar ce da ke da matsalar.

A Kotun Daukaka Kara har ila yau, Gwamnan ya rasa kujerarsa kan matsalar yayin da aka bai wa dan takarar APC, Nentawe Goshwe.

Gwamnan ya bayyana haka ne ga manema labarai a Abuja yayin kai ziyara ga sakataren TETFund, Sonny Echono a Abuja, cewar TheCable.

Wace shawar Caleb ya bayar?

Gwamnan ya godewa ‘yan Najeriya saboda goyon bayan da suka nuna yayin shari’ar inda ya bukaci a yi adalci yadda ya kamata.

Ya ce:

“A karshe ya kamata ayi adalci, ina addu’ar hakan ya zama tsarin ci gaban kasar mu baki daya.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta jingine hukunci kan shari'ar neman tumbuke gwamnan Arewa, NNPP na cikin matsala

“Wannan shi ne tsarin rayuwa, muna sake kira kan yin adalci da daidaito da kuma rashin bambanci, na yi imani Najeriya za ta samu daukaka.”

Gwamna Caleb ya sha da kyar

A wani labarin, Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Muftwang a matsayin zababben gwamnan jihar Plateau.

Kotun ta yi fatali da hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta rusa zaben gwamnan jihar saboda rashin tsari a jam’iyyar PDP a jihar.

A baya kotun ta tabbatar da cewa dan takarar jam’iyyar APC, Nentawe Goshwe ne ya cancanci kujerar gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel