Abin da Atiku Ya Fada Min Bayan Ganawata da Shugaba Tinubu, Bwala

Abin da Atiku Ya Fada Min Bayan Ganawata da Shugaba Tinubu, Bwala

  • Daniel Bwala wanda shi ne tsohon kakakin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku a zaɓen 2023, ya fito ya bayyana yadda suka yi da Atiku bayan ya gana da Tinubu
  • Bwala ya bayyana cewa ya sanar da Atiku kan ganawarsa da Tinubu inda tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce masa ya gode da ya sanar da shi
  • Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa ganawarsa da Shugaba Tinubu ba tana nufin ya ci amanar Atiku ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Daniel Bwala, tsohon kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar a zaɓen 2023, ya ce ya sanar da tsohon maigidan nasa kafin ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu.

Bwala ya gana da Shugaba Tinubu a kwanakin baya, inda suka yi wata ganawar sirri sannan ya bayyana cewa zai yi aiki da gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

"Kwana 7 na yi ban barci": Gwamnan PDP ya fadi yadda cikinsa ya duri ruwa kan hukuncin kotun koli

Bwala ya yi magana kan ganawarsa da Tinubu
Bwala ya kawar da zarfin cin amanar Atiku kan ganawarsa da Tinubu Hoto: Daniel Bwala
Asali: Twitter

A cewarsa, idan har goyon bayan Tinubu na nufin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shirye yake ya koma jam’iyyar ya fice daga jam’iyyar PDP, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Atiku ya gaya wa Bwala?

Da yake magana a shirin Sunday Politics na Channels Tv, Bwala ya bayyana cewa:

“Na sanar da Atiku Abubakar cewa zan gana da shugaban ƙasa. Bayan na gana da shugaban ƙasa, sai na sanar da shi (Atiku) cewa na gana da shugaban ƙasa, sai ya amsa da cewa, ‘Na gode Daniel da ka sanar da ni’."

Bwala ya ce matakin da ya ɗauka na goyon bayan gwamnati mai ci yanzu ba yana nufin ya ci amanar Atiku ba, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Bwala ya musanta cin amanar Atiku

A cewarsa:

"Wannan zancen banza ne wani ya ce saboda na ce zan goyi bayan Shugaba Bola Tinubu saboda haka na ci amanar Atiku."

Kara karanta wannan

"Shi ba dan jihar nan ba ne": Wike ya bayar da karin haske kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Yayin da lauyan ya ƙauracewa fitowa fili ya bayyana jam’iyyarsa a halin yanzu, ya bayyana ƙarara cewa Tinubu bai yi masa alƙawarin samun muƙami ba a ganawar tasu.

Sai dai ya bayyana aniyar yin aiki da shugaban ƙasar a duk wani matsayi da ya dace da muradun al'ummar Najeriya.

Atiku, Obi da Ƙwankwaso Na Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Farfesa Pat Utomi ya bayyana cewa Atiku, Ƙwankwaso da Peter Obi sun shirya kafa sabuwar jam'iyyar haɗaka.

Farfesan wanda masanin siyasa ne ya bayyana cewa ƴan takarar na shugaban ƙasan a zaɓen 2023, sun yanke wannan shawarar ne domin fitowa da ƙarfinsu a zaɓen gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel