Gwamnan PDP Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Bayan Nasararsa a Kotun Koli

Gwamnan PDP Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Bayan Nasararsa a Kotun Koli

  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya nuna farin cikinsa kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke wanda ya tabbatar da nasararsa
  • Gwamnan ya bayyana cewa hukuncin ya nuna cewa ƙasar nan za ta samun daidaito wajen yin abin da dace
  • Kotun ƙolin da ta tabbatar da nasarar gwamnan inda ta soke hukuncin da kotun ƙara ta yanke na tsige shi daga matsayin gwamnan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi magana kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na tabbatar da nasararsa.

Gwamnan a ranar Juma'a ya bayyana cewa hukuncin da kotun ƙolin ta yanke shaida ce kan cewa ƙasar nan za ta iya daidaituwa.

Kara karanta wannan

Gawuna ya yi magana kan hukuncin kotun koli, ya tura muhimmin sako

Gwamna Mutfwang ya yi magana kan hukuncin kotun koli
Gwamna Mutfwang ya nuna jin dadinsa kan hukuncin kotun koli Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Kotun ƙolin mai alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Emmanuel Agim ta sauya hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta kore shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Egim ya ce hukuncin ya zama kauce layi saboda batun zaɓen fidda gwanin da ya haifar da Mutfwang ba hurumin ƙaramar kotun ba ce.

Me gwamnan ya ce kan hukuncin?

Sa’o’i kaɗan bayan yanke hukuncin, gwamnan wanda ya kasance baƙo a gidan talabijin na Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' ya ce ɓangaren shari’a zai daidaita da zarar kotun ƙoli ta yi daidai.

A kalamansa:

"Ya ƙara min da kuzari mai kyau da za mu iya canja tsarin Najeriya. Na kasance mai fatan cewa Najeriya za ta iya canjawa.
"Tare da abin da na gani a kotun ƙoli, ya nuna cewa idan kotun ƙoli za ta iya daidai, tsarin shari'a zai daidaita, gudanar da adalci zai daidaita.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta ƙara yanke hukunci kan sahihancin nasarar gwamnan adawa, PDP ta yi warwas

"Saboda hakan yana nufin za mu mayar da hankali zuwa wajen wasu ɓangarorin ci gaban ƙasarmu. Na yi imanin cewa tare da abubuwa da yawa da ke faruwa a yanzu, da wasu matakan gyara da shugaban ƙasa yake ɗauka, za a samu sauyi."

Gawuna Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Ƙoli

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC, a.jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi martani kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke.

Gawuna ya bayyana cewa ya amince da hukuncin kotun ƙolin wanda ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Asali: Legit.ng

Online view pixel