Atiku Ya Faɗi Shirinsa Na Gaba Kan Tinubu da APC Bayan Gwamnoni 4 Sun yi Nasara a Kotun Ƙoli

Atiku Ya Faɗi Shirinsa Na Gaba Kan Tinubu da APC Bayan Gwamnoni 4 Sun yi Nasara a Kotun Ƙoli

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana matakin da zai ɗauka kan APC da Shugaba Tinubu a 2027
  • Atiku ya ce ya kudiri aniya tare da shirya jagorantar gamayyar jam'iyyun adawa da zasu kawar da APC da Tinubu daga kan mulki
  • A cewarsa, nasarar da gwamnonin jam'iyyar PDP suka samu a kotun koli nasara ce ga tsarin demokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi magana kan nasarar gwamnoni a kotun koli.

Atiku ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin jan ragamar gamayyar jam'iyyun adawa wajen yaƙar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da APC mai mulki a 2027.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban NNPP ya faɗi gaskiyar wanda zai samu nasarar tsakanin Abba da Gawuna a kotun koli

Atiku Abubakar da Shugaba Tinubu.
Atiku Ya Faɗi Shirinsa Kan Tinubu Bayan Gwamnonin PDP Sun Yi Nasara a Kotum Koli Hoto: Atiku Abubakar/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce haɗin kai da majar ƴan adawa ne kaɗai zai kara danƙon demokuraɗiyya a Najeriya, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Atiku ya bayyana haka ne a saƙon taya murna da ya aike wa gwamnonin jam'iyyar PDP, waɗanda kotun koli ta tabbatar masu da nasara ranar Jumu'a, 12 ga watan Janairu.

A sanarwan da ofishinsa na midiya ya fitar a Abuja, Atiku ya ce:

"A shirye nake kamar yadda aka saba na jan ragama gwamnonin mu da sauran jagororinmu domin ci gaban ƙasar nan."
"Duk inda muka ga an yi adalci sosai, mu, a matsayinmu na masu kishin kasa kuma 'yan kasa, za mu yaba."

Gwamnonin PDP sun samu nasara a kotun koli

Wannan kalamai nasa na zuwa ne a ranar da kotun koli ta yanke hukunci kan zaben gwamnonin jihohin Bauchi, Zamfara, da Filato.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana gwamnoni da 'yan majalisun tarayya da za su rungumi jam'iyyar APC

Kotun ta tabbatatar da nasarar Bala Muhammed na Bauchi, Dauda Lawal na Zamfara da kuma Celeb Mutfwang na jihar Filato, dukkansu mambobin PDP.

Hakan ya zo ne awanni 24 bayan kotun mai daraja ta ɗaya ta tabbatar da nasarar Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom a zaben 18 ga watan Maris, The Nation ta ruwaito.

Kotun koli ta raba gardama kan zaben Abia

A wani rahoton kuma Kotun koli ta yanke hukunci kan ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna suka kalubalanci nasarar gwamnan Abia.

A zaman yanke hukuncin yau Jumu'a, 12 ga watan Janairu, kotun ta kori ƙarar gaba ɗaya bisa rashin cancanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel