Wasu ‘Yan Arewa Sun Shiga Kitsa Yadda Za a Canza Ganduje a Matsayin Shugaban APC

Wasu ‘Yan Arewa Sun Shiga Kitsa Yadda Za a Canza Ganduje a Matsayin Shugaban APC

  • Har zuwa yau, ba a sa ranar da majalisar kolin jam’iyyar APC watau NEC za tayi zama a Najeriya ba
  • Ana tunanin wasu jagororin APC daga Arewa ta tsakiya ba su hakura da kujerar shugaban jam’iyya ba
  • An yi watsi da yankin a lokacin da Abdullahi Adamu ya sauka, aka dauko Abdullahi Umar Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki sun fara tunanin yadda za a canza Abdullahi Umar Ganduje a majalisar NWC.

Duk da Dr. Abdullahi Umar Ganduje bai kai shekara guda a ofis ba, Daily Trust ta ce akwai ‘yan siyasan da ke harin kujerarsa.

Ganduje = APC
Abdullahi Ganduje tare da jagororin APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Wasu ba su so kawo Abdullahi Ganduje ba

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi shagube ga Betta kan alkawarinta na fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

Tun farko mutanen Arewa maso tsakiya ba su ji dadin yadda tsohon gwamnan na Kano ya gaje kujerar Abdullahi Adamu a APC ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan siyasar yankin sun yi tunani daga cikinsu za a dauko sabon shugaban jam’iyya na kasa sa’ilin da Sanata Adamu ya yi murabus.

Majiyoyi sun shaidawa jaridar jiga-jigai daga Arewa ta tsakiya sun shiga lissafin yadda kujerar shugaban APC za ta dawo masu.

Ganduje: APC tayi watsi da tsarinta

Bayan Bola Tinubu ya zama mulki, an yi watsi da tsarin da aka saba bi wajen maye gurbin shugabannin da su ka bar majalisar NWC.

A lokacin da aka yi waje da John Odigie Oyegun, daga jiharsa ta Edo aka dauko magajinsa watau Adams Oshiomhole a shekarar 2018.

Hakan ta faru da aka tashi nada Ajibola Basiru a sakatare bayan Iyiola Omisore kamar yadda Abiola Ajimobi ya gaji Niyi Adebayo.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar ICPC ya zo da sabon salon yaki da cin hanci wanda ba a taba gani ba a Najeriya

Bayan rasuwar Abiola Ajimobi, legit ta fahimci daga kudu maso yamma APC ta kawo wanda zai zama mataimakin shugaba na kasa.

Yadda aka saba doka wajen nada Ganduje

Haka zalika rahoton ya ce an yi watsi da dokar APC da aka nada Abdullahi Ganduje ba tare da an kira taron zaben shugabanni ba.

Amma wasu suna gani zai yi wahala na kusa da shugaban kasa su bari a taba Ganduje musamman yadda ake hangen zaben 2027.

Majiyoyi sun tabbatar da Yahaya Bello ake tunani za a kawo ya canji Abdullahi Ganduje. Bello bai nuna yana neman matsayin ba.

Wa’adin Mai girma gwamnan jihar Kogi zai kare a karshen watan nan, bayan ya yi shekaru takwas yana mulki daga 2015 zuwa 2023.

APC tana son dauke Nyesom Wike

Ana da labari jam’iyyar APC ta tuntubi masu addu’o’i da yawa domin a canzawa Nyesom Wike shawara ya fice daga PDP mai adawa.

Jagoran jam’iyya mai mulki a Kudancin Najeriya, Cif Victor Giadom yana so su karasa yi wa jam'iyyar PDP illa, a raba ta da Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel