Shugaban Hukumar ICPC Ya Zo da Sabon Salon Yaki da Cin Hanci Wanda Ba A Taba Gani Ba a Najeriya

Shugaban Hukumar ICPC Ya Zo da Sabon Salon Yaki da Cin Hanci Wanda Ba A Taba Gani Ba a Najeriya

  • Za a ga sabon canji kan yadda hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ke gudanar da ayyukanta a Najeriya
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban hukumar, Musa Aliyu ya bayyana cewa shi da kansa zai riƙa zuwa kotu domin kare ƙararrakin hukumar
  • Musa ya yi nuni da cewa yaƙi da hanci sai an yi masa taron dangi domin a samu a kawar da shi daga ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, Musa Aliyu, ya ce zai riƙa zuwa gaban kotu domin kare shari’o’in da suka shafi hukumar.

Shugaban wanda shine babban lauyan jihar Jigawa kafin a nada shi a matsayin shugaban hukumar ICPC, ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, cewar rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Bayan kama 8, Asirin masu hannu a kisan bayin Allah sama da 150 ya ƙara tonuwa a arewa

Shugaban ICPC ya zo da sabon salo
Shugaban ICPC zai rika kare kararrakin hukumar a gaban kotu Hoto: @icpcnigeria
Asali: Twitter

Aliyu ya bayyana cewa zai yi jagorancu wanda zai zama abun koyi a saura.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Zan zama jagora. Da yardar Allah na yi niyyar zuwa shari’ar ICPC a kotu. Ba na jin an taɓa samun shugaban ICPC da ya bayyana a kotu, amma ni ne na farko.
"Na himmatu matuƙa wajen ganin an cimma manufa ta Nijeriya inda ƙa’idojin gaskiya, riƙon amana, da bayyana gaskiya za su ratsa jikin al'ummar mu."

Musa ya kuma ƙara da cewa yaki da cin hanci da rashawa na buƙatar haɗa kai, da bangarori da dama, domin ya wuce ƙarfin ƙungiya ɗaya.

Yaushe zai riƙa zuwa kotun?

Jaridar Leadership ta ce shugaban ya ce zai riƙa zaɓar ƙararrakin da ya ga ya kamata ya wakilci hukumar, ko kuma ya ba wasu manyan jami'an hukumar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da binciken Betta Edu, shugaban EFCC ya aike da sabon gargadi

Sai dai, ya ce duk da dokar kafa hukumar ta ba shi damar yin hakan, Antoni Janar na ƙasa na da ikon hana shi, saboda duk wasu masu bincike na gwamnatin tarayya shi ne yake amincewa da su.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sa masu ruwa da tsaki daban-daban da suka haɗa da kafofin watsa labarai, sauran hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, ƙungiyoyin farar hula da sauransu domin kawo ƙarshen matsalar.

Ya kuma ƙara da cewa yaki da cin hanci da rashawa na ICPC daga yanzu zai dogara ne akan amfani da fasahar wajen hanzarta tafiyar da lamarin.

Shugaban ICPC Ya Gana da Umar Audu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar ICPC, Musa Aliyu, ya gana da ɗan jaridar nan Umar Shehu Audu.

Umar Shehu Audu dai shi ne ɗan jaridan da ya bankaɗo yadda ake samun digirin bogi cikin sauƙi a Jamhuriyar Benin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel