Tsohon Ministan Tinubu Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki a Matsayin Sanata

Tsohon Ministan Tinubu Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki a Matsayin Sanata

  • Tsohon Ministan Kwadago a Najeriya, Simon Lalong ya yi murabus daga kujerarshi ta Minista a wannan makon
  • Lalong ya yi murabus din ne bayan ya yi nasara a Kotun Daukaka Kara kan shari'ar zaben sanata a Plateau ta Kudu
  • Da safiyar yau Laraba ce Lalong ya karbi rantsuwar kama aiki a Majalisar Dattawa a matsayin Sanata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya kama rantsuwar kama aiki a matsayin Sanata a jihar.

Lalong wanda shi ne tsohon Ministan Kwadago ya karbi rantsuwar ce a dakin Majalisar Dattawa a yau Laraba 20 ga watan Disamba a Abuja.

Tsohon gwamna ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin sanata
Majalisar Dattawa ta rantsar da tsohon Minista Lalong a matsayin Sanata. Hoto: Simon Lalong.
Asali: Facebook

Yaushe aka rantsar da Lalong a Majalisa?

Kara karanta wannan

Harin sojojin Najeriya kan farar hula: Miyetti Allah ta kafa wa Tinubu wani muhimmin sharadi

A ranar Talata, hadimin tsohon gwamnan, Simon Macham ya bayyana haka inda ya ce Lalong ya yi murabus daga kujerar Minista, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani, Shugaba Tinubu ya tabbatar da karbar takardar yin murabus din Sanatan da ke wakiltar Plateau ta Kudu, cewar Leadership.

Tinubu ya karbi takardar murabus din ne a ranar Litinin 18 ga watan Disamba inda rahotanni su ka tabbar cewa bai ji dadin murabus din ba.

Yaushe Lalong ya karbi satifiket na cin zaben Sanata?

A ranar 23 ga watan Nuwamba ce Lalong ya karbi satifiket da ke tabbatar da nasararshi a matsayin sanatan da ke wakiltar Plateau ta Kudu a Majalisa.

Lalong da sauran masoyansa sun ziyarci ofishin hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da ke Abuja don karbar satifiket din.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya dauko hanyar hana Shoprite barin Kano

Kwamishinan hukumar zabe ta kasa, Mohammed Haruna shi ya mika satifiket din ga tsohon gwamnan jihar Plateau tare da dandazon masoyansa.

Jiga-jigan APC da ke neman kujerar Lalong

A wani labarin, Bayan tsohon gwamnan jihar Plateau ya yi murabus daga kujerar Minista, wasu manyan APC a jihar na neman gadar kujerar.

Lalong ya ajiye mukamin Minista ne bayan ya yi nasara a Kotun Daukaka Kara a matsayin sanatan Plateau ta Kudu.

Kafin ajiye kujerar ta shi, tsohon gwamnan shi ne Ministan Kwadago da ayyuka wanda Tinubu ya nada shi farkon hawanshi mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel