A Karshe: Simon Lalong Ya Ajiye Mukamin Minista da Tinubu Ya Bashi, an Samu Cikakkun Bayani

A Karshe: Simon Lalong Ya Ajiye Mukamin Minista da Tinubu Ya Bashi, an Samu Cikakkun Bayani

  • Simon Lalong ya bar majalisar ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a hukumance domin ya karbi kujerar sa ta majalisar dattawa
  • Tsohon gwamnan Filato ya mika takardar yin murabus a makon da ya gabata, kuma shugaba Tinubu ya amince da hakan
  • Wannan lamari dai na zuwa ne bayan Kotun Daukaka Kara ta bayyana Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanatan Filato ta Kudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja – Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong, ya yi murabus a hukumance, wanda ke nuni da ficewa daga mamba a majalisar ministocin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

Lalong, tsohon gwamnan jihar Filato, ya zabi zama dan majalisar dattawan Filato ta Kudu bayan hukuncin kotu da ta ba shi nasara a zaben da ya gabata.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

Tinubu ya amince da murabus din Lalong
Ana sa ran shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio zai rantsar da Lalong a cikin wannan mako. Hoto: Bola Ahmed Tinubu/Simon Lalong
Asali: Facebook

Ana sa ran shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio zai rantsar da Lalong a cikin wannan mako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya amince da murabus din Lalong

Duk da cewa tun farko INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Fabrairu, Lalong ya shigar da kara kan sakamakon zaben inda a karshe ya samu nasara a Kotun Daukaka Kara.

Lalong ya mika takardar murabus dinsa ne a ranar Larabar da ta gabata a daidai lokacin da yake shirin karbar sabon mukaminsa a majalisar dokokin kasar.

An tabbatar da murabus din Lalong ta hanyar wani sako a shafin X, wanda wani mai taimaka wa shugaban kasa Imran Muhammad, ya rubuta kamar haka:

“Shugaba Tinubu ya amince da murabus din ministan kwadago da samar da ayyuka, Simon Lalong daga majalisar ministoci."

Kara karanta wannan

Akpabio na cikin wani yanayi bayan zargin ya fadi yayin bikin ranar haihuwarsa, bayanai sun fito

INEC ta mika takardar shaidar nasara ga Lalong

A watan da ya gabata ne dai Gwamna Lalong ya samu takardar shedar nasarar cin zabe sakamakon umarnin da Kotun Daukaka Kara ta baiwa hukumar zaben.

Hakan ya biyo bayan soke zaben Air Vice Marshall Napoleon Bali daga jam'iyyar PDP, lamarin da ya sa Lalong ya dare kujerar sanatan.

A ziyarar da ya kai hedikwatar INEC, Lalong ya samu rakiyar iyalansa da suka hada da matarsa ​​Regina da ‘ya’yansa, da wasu jigogin jam'iyyar APC.

Jami'a na kashe wa kowanne dalibin likitanci N5bn a Najeriya

A wani labarin, jami'o'in Najeriya sun koka kan karancin kudin da suke samu don gudanar da ayyukan horas da dalibai, musamman na fannin likitanci a kasar.

Kwamitin shugabannin jami'o'i CVCNU ya yi wannan korafin, inda ya yi nuni da cewa kowanne dalibin likitanci na lakume naira biliyan biyar, rahoton Legit Hausa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel