Kwankwasiyya da Gandujiyya da Sauran Rigingimun Siyasar da Suka fi Dadewa a Najeriya

Kwankwasiyya da Gandujiyya da Sauran Rigingimun Siyasar da Suka fi Dadewa a Najeriya

  • Akwai jihohin da an dauki shekaru maso tsawo, ana gwabza rikicin siyasan da har yau ya ki zuwa karshe
  • Tun 2003 ake gaba tsakanin magoya bayan Rabiu Kwankwaso da na Malam Ibrahim Shekarau a Kano
  • Duk shekarun nan, Bode George yana yakar Bola Tinubu a Legas amma PDP ba ta iya tabuka abin kirki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

1. Kwankwaso v Shekarau

Rabiu Kwankwaso ya gaza samun tazarce a zaben 2023 ne a dalilin Ibrahim Shekarau. Jam'iyyar ANPP ta hana tsohon gwamnan dawowa mulki sai 2011.

Bayan Kwankwaso ya ci zabe a 2011, shi da Ibrahim Shekarau sun zauna tare a APC kafin Malam ya sauya-sheka zuwa PDP, jam’iyyar da ta sake hada su a 2018.

Shekarau ya sake rabuwa da Kwankwaso har ya gaje kujerarsa a 2019, da APC ta yi masa zafi, sun zauna tare a jam’iyyar NNPP kafin kowanensu ya sake jan daga.

Kara karanta wannan

Abba, Caleb da Gwamnonin Jihohi 13 da za a yi shari’ar zaben 2023 da su a Kotun Koli

Kwankwasiyya da Gandujiyya
Rigimar 'yan siyasan Najeriya Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR da Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Kwankwaso v Ganduje

Tun 2016 alamu su ka fara nuna an samu rashin jituwa tsakanin Abdullahi Ganduje da tsohon mai gidansa, wanda ya yaki tazarcensa karara lokacin zaben 2019.

A zaben 2023, Abdullahi Ganduje bai iya samun yadda yake so a Kano ba. ‘Dan takaran Kwankwaso a NNPP, Abba Kabir Yusuf ne ya doke APC a zaben da aka yi.

Daga baya an ji yadda Dr. Ganduje ya samu shugabancin jam'iyyar APC na kasa.

3. Bafarawa v Wammako

Attahiru Bafarawa bai goyi bayan mataimakinsa ya gaje shi da zai bar ofis ba, amma bai iya hana Aliyu Wammako zama gwamnan jihar Sokoto a Mayun 2007 ba.

Bayan Wammako ya tsallake duk wasu tarkon tsohon gwamna sai ya zama Sanata. Dukkansu biyun sun hadu da aka kafa APC kafin Bafarawa ya canza sheka.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta daina boye-boye, tayi wa Ministan Tinubu tayin da zai jawo ya bar PDP

Har gobe Sanatan jagora ne a APC shi kuma Bafarawa yana cikin manyan ‘yan PDP.

4. Amaechi v Wike

Rotimi Amaechi ya dare mulki ne a sakamakon hukuncin kotu, da ya zama Gwamna sai ya dauko Nyesom Wike ya zama shugaban fadar gwamnatin Ribas.

Zuwa lokacin da Wike ya samu mukamin Minista, sabaninsa da Amaechi ya fito fili. Kafin ayi nisa Gwamnan ya koma APC, shi Ministan ya samu takara a PDP.

A zaben 2015 APC ta karbi mulkin kasa shi kuma Wike ya zama Gwamna. Gabar ‘yan siyasar tayi tasiri a zaben bana, har yau kuma ba a ga maciji da juna.

5. Jonathan v Sylva

Timipre Sylva ya zama gwamna da Goodluck Jonathan ya samu takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2007, amma wa’adi guda kurum ya yi a ofis.

Ana zargin Sylva ya samu matsala da shugaba Goodluck Jonathan, saboda haka PDP ta hana shi tikitin tazarce lokacin zaben 2011, aka tsaida Seriake Dickson.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

Tsohon gwamnan ya tsira da kujerar Minista daga baya, ko da ya sake neman takarar gwamna a APC a 2023, gabansa da Dr. Jonathan ta bayyana karara.

6. George v Tinubu

Wata rigima da aka gagara kashe wutanta na tsawon shekara da shekaru ita ce ta Bode George da Bola Ahmed Tinubu a karkashin jam’iyyun PDP da APC.

Duk da George bai taba samun galaba a kan Bola Tinubu a Legas ba, gabar ba ta lafa ba bayan jigon na PDP ya ce zai bar Najeriya idan aka rantsar da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel