Kwankwaso ya bi Shekarau har gida, ya ba shi takarar Sanatan da ta canza lissafin 2023

Kwankwaso ya bi Shekarau har gida, ya ba shi takarar Sanatan da ta canza lissafin 2023

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya zama aminin tsohon abokin gabansa a harkar siyasa, Ibrahim Shekarau
  • Har gida Kwankwaso ya je wajen Malam Shekarau domin ya gabatar masa da fam din neman Sanata
  • Sanata Shekarau ya samu tikiti a bagas kamar yadda aka yi da ya fice daga PDP zuwa APC a 2018

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya je har gida ya kai Malam Ibrahim Shekarau fam din neman takarar Sanata a NNPP.

A ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2022, jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya taka har gidan Sanatan domin ba shi fam.

Kwankwaso ya ajiye gabar da ke tsakaninsa da Malam Shekarau bayan Sanatan na Kano ta tsakiya ya shigo jam’iyyar hamayya ta NNPP mai kayan dadi.

Kara karanta wannan

Allah ne ya aiko Kwankwaso ya fatattaki yunwa, ya hada kan 'yan Najeriya, NNPP

Kafin yanzu Shekarau da Kwankwaso na wasan bera da mage ne a siyasa. A duk lokacin da wannan ya shiga wata jam’iyya, sai dayan ya fice daga cikinta.

Gabanin zaben 2019 Shekarau ya bar PDP bayan dawowar 'Yan Kwankwasiyya. A karshe ya shiga APC wanda ta ba shi takarar ‘dan majalisar dattawa a saukake.

A wancan lokaci akwai wasu na kusa da Gwamna Abdullahi Ganduje masu son kujerar, amma suka hakura. Kafin a je ko ina aka samu baraka a tafiyar APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwankwaso da Shekarau
Malam Ibrahim Shekarau a jam'iyyar NNPP Hoto: Saifullahi Hassan, @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Za a zarce a Kano ta tsakiya?

Auren da aka yi tsakanin tsofaffin gwamnonin a jam’iyya mai kayan marmari yana nufin Ibrahim Shekarau ya samu damar zarcewa a kujerar Sanatan tsakiya.

A tarihin wannan kujera babu wanda ya taba yin tazarce, NNPP za ta ba Sardauna wannan dama.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Shekarau ya karbi katinsa na zama cikakken dan jam’iyyar NNPP

Kafin yanzu wadanda suka rike kujerar a baya, Rabiu Kwankwaso, Bashir Garba, Rufai Hanga, Mohammed Bello ba su zarce bayan wa’adinsu na farko ba.

Idan Shekarau ya samu tikiti a NNPP, zai hadu da wanda APC ta ba takara tsakanin Bashir Garbo, A. A Zaura da Abdullahi Ramat daga jam'iyyar APC mai mulki.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa daga PDP akwai irinsu Laila Buhari da ke neman takarar Sanata. Ana rade-radin Abubakar Nuhu Damburam ya sauya-sheka.

Aliyu Madakin Gini ya sallama

Kamar yadda Hon. Aliyu Sani Madakin Gini ya bayyana a shafinsa na Facebook, ya amince da matakin da jagororin NNPP suka dauka na tsaida Shekarau.

Tsohon ‘dan majalisar shi ne ya yi takarar Sanatan tsakiyar Kano a PDP a zaben 2019, a nan ma ya sha kashi ne wajen Shekarau wanda shi ya rike tutar APC.

Wani 'dan Kwankwasiyya ya shaida mana cewa a baya an yi tunani jam’iyyar za ta tsaida Rufai Hanga ko Aliyu Madaki ne a matsayin ‘dan takarar Sanata.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shekarau ya dawo jam'iyyar mu, kwankwaso ya taya shi murna, NNPP

Akwai yiwuwar idan aka tafi a haka, Madaki ya dawo ya yi takarar kujerar ‘dan majalisar Dala. Kafin yanzu ya rike wannan kujera har zuwa Mayun 2019.

Mu na da labari Injiniya Muhammad Mahbub Ibrahim da Lawal Husseini su na cikin wadanda suka saye fam domin yin takarar majalisar tarayya a NNPP.

Jawabin Aliyu Madaki a Facebook

Alhamdulillahi Ala Kullu Halin.
Ina Amfani da wannan yanayi,in mika sakon godiya ga dukkan masoya da magoya baya,bisa goyon baya da kyauna da aka nuna mun akan takarar Sanata dana nemi.Allah cikin ikon Sa,bamu samu ba,muna godiya da Allah.Ina godiya ga Allah abunda Ya bani.Alhamdulillah.
Allah Ya saka,Allah Yabar zumunci.
Allah Alhamdulillah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel