Gwamnan PDP Ya Bada Mamaki Kwana Ɗaya Bayan Miƙa Kasafin Kuɗin 2024 Ga Majalisa

Gwamnan PDP Ya Bada Mamaki Kwana Ɗaya Bayan Miƙa Kasafin Kuɗin 2024 Ga Majalisa

  • Gwamna Fubara na jihar Ribas ya rattaɓa hannu a kasafin kuɗin 2024 awanni 24 bayan gabatar da shi a majalisar dokoki
  • A yanzu kasafin ya zama doka bayan sa hannun gwamnan ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba a wani taro a gidan gwamnati
  • Da yake jawabi, Fubara ya ce kasafin zai maida hankali wajen gina ayyukan more rayuwa da samar wa matasa ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya rattaɓa hannu kan kudirin kasafin kuɗin shekarar 2024 na N800bn ya zama doka.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Gwamna Fubara ya rattaɓa hannu kan kasafin ne a wani ɗan kwarya-kwaryar biki da aka shirya a gidan gwamnati da ke Patakwal.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Aiyedatiwa ya kama aiki a matsayin mukaddashin gwamnan Ondo

Gwamna Fubara ya sa hannu a kasafin 2024.
Gwamna Fubara na jihar Rivers ya rattaba hannu a kasafin kuɗin 2024 Hoto: Sim Fubara
Asali: Facebook

Bikin ya gudana ne a ɗakin taro na ofishin gwamnan jihar Ribas ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin majalisar dokokin jihar Ribas wanda kotu ta tabbatar, Edison Ehie, shi ne ya jagoranci ƴan majalisa huɗu suka amince da ƙunshin kasafin kuɗin na 2024.

A ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023 Gwamna Fubara ya gabatar da kasafin ga majalisa kuma cikin abinda bai haura sa'o'i 24 majalisar ta amince.

A rahoton Channels tv, bikin sa hannu kan kasafin kuɗin ya samu halartar mataimakin gwamna, Farfesa Ngozi Odu, da wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwa.

Haka nan wasu ƴan majalisa masu ci da tsofaffi waɗanda ke goyon bayan Gwamna Fubara da shugabannin Peoples Democratic Party (PDP) na ƙananan hukumomi sun halarci wurin.

Zamu zuba ayyukan more rayuwa - Fubara

Kara karanta wannan

Rikicin Wike da Fubara ya dauki sabon salo yayin da atoni janar na Ribas ya yi murabus

A jawabinsa, Gwamnan ya ce kasafin Naira biliyan 800 da aka yi wa lakabi da, ‘Budget of Renewed Hope, Consolidation and Continuity’ za a aiwatar da shi sosai don samar da muhimman ababen more rayuwa.

A nasa bangaren, Edison Ehie, daya daga cikin wadanda ke rigima kan kujerar kakakin majalisar dokokin jihar Ribas, ya yabawa hangen nesan gwamnan.

A cewarsa, Gwamnan ya nuna ƙwarewa a kasafin, inda ya kudiri aniyar fadada abubuwan more rayuwa da ci gaban matasa ta hanyar samar da ayyukan yi.

Aiyedatiwa ya kama aiki a ofishin gwamna

A wani rahoton na daban Mataimakin Gwamna Rotimi Akeredolu ya koma jihar Ondo ranar Laraba kuma ya kama aiki a matsayin muƙaddashin gwamnan jihar.

Lucky Aiyedatiwa ya samu kyakkyawar tarba daga magoya bayansa yayin da ya sauka a filin jirgin sama na Akure, babban birnin Ondo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel