Murna Yayin da Aiyedatiwa Ya Kama Aiki a Matsayin Mukaddashin Gwamnan Ondo

Murna Yayin da Aiyedatiwa Ya Kama Aiki a Matsayin Mukaddashin Gwamnan Ondo

  • Mataimakin Gwamna Rotimi Akeredolu ya koma jihar Ondo ranar Laraba kuma ya kama aiki a matsayin muƙaddashin gwamnan jihar
  • Lucky Aiyedatiwa ya samu kyakkyawar tarba daga magoya bayansa yayin da ya sauka a filin jirgin sama na Akure, babban birnin Ondo
  • Legit Hausa ta fahimci a halin yanzu shi ne zai ci gaba da jan ragamar harkokin mulkin Ondo yayin da Gwamna ke jinyar rashin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Muƙaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya shiga ofis, y kama aiki gadan-gadan a matsayin muƙaddashin gwamna.

Kamar yadda jaridar The Nation ta tattaro, muƙaddashin gwamnan ya shiga ofis ne jim kaɗan bayan ya koma Akure, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bada mamaki kwana daya bayan miƙa kasafin kuɗin 2024 ga majalisa

Mukaddashin gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa.
Murna Yayin da Aiyedatiwa Ya Kama Aiki a Matsayin Mukaddashin Gwamnan Ondo Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Mista Aiyedatiwa ya samu kyakkyawar tarba daga tsohon sakataren gwamnatin jihar Ondo, Ifedayo Abegunde, tare da ɗumbin magoya bayansa ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Akeredolu ya tafi hutu karo na biyu

Jaridar Punch ta rahoto cewa tun da farko dai majalisar dokokin jihar Ondo ta tabbatar da Lucky Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamna.

Hakan ya biyo bayan samun wasiƙa daga Gwamna Rotimi Akeredolu. wanda ya sanar da majalisar cewa zai sake tafiya hutun jinyar rashin lafiya a karo na biyu.

Shugaban majalisar, Olamide Oladiji, ya ce matakin da Gwamnan ya ɗauki ya yi daidai da tanadin sashi 190 da ke ƙunshe a kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 wanda aka yi wa garambawul.

A wasiƙar, Gwamnan wanda ke fama da rashin lafiya ya sanar da majalisar cewa Aiyedatiwa zai karɓi ragamar mulki a matsayin muƙaddashi har sai ya sake turo takardar da ta saɓa wa haka.

Kara karanta wannan

"Ina da tarin ilimi": Tsohon shugaban daliban jami'ar UNIBEN ya tsaya takarar gwamna a jihar Edo

Ya kuma bayyana cewa sabon hutun da ya ɗauka zai fara ne daga ranar 13 ga watan Disamba.

Nan da nan dai aka ga magoya bayan mataimakin gwamnan suka fara murna da farin ciki a kafafen sada zumunta.

Gwamnan APC Ya Nada Sabbin Hadimai Sama da 150

A wani rahoton na daban Gwamna Biodun Oyebanji ya yi sabbin naɗe-naɗen hadiman da zasu kama masa wajen tafiyar da harkokin shugabanci a jihar Ekiti.

Gwamna Oyebanji ya naɗa akalla manyan masu taimaka masa (SSA) guda 79, kananan masu taimaka masa (SA) 73 da masu ba shi shawara 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262