Sanatan PDP a Arewa Ya Gwangwaje 'Yan Yankinsa da Mukaman Masu Ba Shi Shawara 64, Ya Fadi Dalili

Sanatan PDP a Arewa Ya Gwangwaje 'Yan Yankinsa da Mukaman Masu Ba Shi Shawara 64, Ya Fadi Dalili

  • Sanatan Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal ya nada sabbin hadimai guda 64 da za su taimaka masa a harkokin gudanarwa
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Muhammad Bello, hadiminsa a bangaren yada labarai ya fitar a yau Litinin 11 ga watan Disamba
  • Tsohon gwamnan ya ce ya nada hadimin ne don taimaka masa a ayyuka da kuma tallafawa 'yan yankin wurin samun saukin gudanar da mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya nada sabbin hadimai 64 a mazabarshi da ke jihar Sokoto.

Tsohon gwamnan ya nada sabbin hadimai ne a mazabar Sokoto ta Kudu don tallafawa 'yan yankinsa, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Cikakken sunayen jiga-jigan APC da ke dakon kujerar Minista Lalong idan ya koma sanata

Sanata Tambuwal ya nada hadimai guda 64 a mazabarshi, ya fadi dalili
Sanata Aminu Tambuwal ya nada hadimai guda 64 a mazabarshi. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal.
Asali: Facebook

Yaushe Sanata Tambuwal ya yi sabbin nade-naden?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Muhammad Bello, hadiminsa a bangaren yada labarai ya fitar a yau Litinin 11 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello ya ce daga cikin wadanda suka samu mukamin sun hada tsaffin kwamishinoni da hadimai na Sanatan lokacin da ya ke gwamna, cewar Tribune.

Daga cikin wadanda su ka samu mukamin sun hada da:

1. Aminu Bodinga, bangaren harkokin mazaba.

2. Alhaji Ahmed Maradu, bangaren harkokin siyasa.

3. Bala Yabo, bangaren jin dadi

4. Bello Tureta, bangaren harkokin addini da masarautun gargajiya.

5. Nasiru Tambuwal, bangaren Matasa da dalibai.

6. Bashir Lambara, bangaren ayyuka na musamman

7. Lauwali Fakku, bangaren wayar da kan jama'a.

8. Abdullahi Dange, bangaren tsaro.

Wasu daga cikin wadanda Tambuwal ya nada mukamin

Punch ta tattaro cewa sauran wadanda ba a bayyana ofisoshinsu ba sun hada da:

Kara karanta wannan

Sanatoci sun burge, sun ba da albashinsu gaba daya ga 'yan maulidin da harin soji ya shafa

1. Lauwali Ubandoma

2. Surajo Isah

3. Ibrahim Ubale

4. Haliru Kilgori

5. Abubakar Rafi

6. Abubakar Salihu

7. Ummaru Bodinga.

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar Tambuwal

A wani labarin, kotun zabe ta tabbatar da nasarar Sanata Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP a jihar Sokoto a matsayin zababben Sanata.

Tambuwal ya yi nasara ne a matsayin sanatan Sokoto ta Kudu a zaben da aka gudanar a watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel