Kotu Ta Tabbatar da Nasarar Tambuwal a Matsayin Sanatan Sokoto Ta Kudu
- Kotun zaɓe ta tabbatar da nasarar Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP a zaɓen Sanatan Sokoto ta kudu
- Ɗan takarar APC, Abdullahi Ɗanbaba ne ya kalubalanci sakamakon zaben da INEC ta bayyana bisa zargin saɓa doka
- Sai dai Kotu ta yi fatali da ƙarar a zaman yanke hukunci ranar Laraba saboda rashin cancanta
Jihar Sokoto - Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta jihar Sakkwato ta tabbatar da nasarar tsohon gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal a zaɓen Sanatoci na 2023.
Kotun zaɓe ta tabbatar da Tambuwal a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen Sanata jihar Sakkwato ta kudu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Tun da farko, ɗan takarar jam'iyyar APC, Abdullahi Danbaba, ya kai ƙara gaban Kotun inda ya kalubalanci nasarar Aminu Tambuwal na PDP, Channels tv ta ruwaito.
Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Bayan INEC Ta Cire Sunan Dan Takararta a Cikin Jerin Yan Takarar Gwamnan Bayelsa
Ɗanbaba ya roƙi Kotun da ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba saboda rashin bin ka'idojin dokar zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bukaci kotun da ta bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 28 waɗanda yake zargin ba a gudanar da zaben ba a zaɓe watan Fabrairu da ƙarishen da aka yi a watan Afrilu.
Kotu ta yanke hukunci
Da take yanke hukunci, Kotun ta yi watsi da karar saboda rashin cancanta, tana mai cewa takardun shaidun da mai ƙara ya gabatar ba su da inganci.
Kotun ta kuma umarci mai ƙara ya biya waɗan da ake tuhuma na ɗaya daga biyu Naira N200,000 kowanensu watau Sanata Tambuwal da kuma jam'iyyar PDP.
Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Sokoto wanda ya shafe zango biyu a kan mulki, ya lashe zaben Sanatan Sokoto ta kudu da kuri’u 100,860.
Da tazarar kuri’u 4,976, ya doke abokin hamayyarsa Danbaba wanda ya samu kuri’u 95,884, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Kotu Ta Tsige Sarkin Masarautar Ogbomoso
A wani rahoton na daban kuma Babbar Kotun Oyo, a ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, 2023, ta rushe naɗin Sarki watau Soun na Ogbomoso, Oba Ghandi Olaoye.
Gwamnatin jihar Oyo ce ta amince da naɗin sabon Sarkin wanda aka yi bikin naɗa masa rawanin Sarauta ranar 8 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng