Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama Kan Karar Da Ke Neman Tsige Gwamnan PDP a Arewa

Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama Kan Karar Da Ke Neman Tsige Gwamnan PDP a Arewa

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar da Gwamna Agbu Kefas na jam'iyyar PDP ya samu a zaɓen gwamnan jihar Taraba na ranar 18 ga watan Maris
  • Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar NNPP da ɗan takararta Sani Yahaya suka shigar suna ƙalubalantar nasarar Gwamna Kefas
  • Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun zaɓe na yin watsi da ƙarar inda ta yi nuni da cewa ƙarar ba ta cancanta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da Sani Yahaya na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya shigar da ke ƙalubalantar zaɓen ɗan takarar jam’iyyar PDP Kefas Agbu a matsayin gwamnan jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Tsige gwamnan Kano: Bode George ya caccaki hukuncin kotun daukaka kara

Yahaya da jam’iyyarsa sun ƙalubalanci sakamakon zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris bisa dalilan rashin bin dokar zaɓe, inda suka bayyana cewa Agbu bai samu rinjayen ƙuri’un da aka kaɗa ba.

Kotu ta tabbatar da nasarar Agbu Kefas
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Agbu Kefas Hoto: Agbu Kefas, Court of Appeal Nigeria
Asali: Twitter

Meyasa kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Kefas?

A hukuncin bai ɗaya da ta yanke, kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar NNPP ta shigar kan rashin cancanta kamar yadda kotun zaɓe ta yi a ranar 30 ga watan Satumba, cewar rahoton Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kotun mai shari'a Peter Affen a yayin yanke hukuncin, ya yi nuni da cewa da masu ɗaukaka ƙarar sun kasa kawo ƙwararan hujjoji kan ƙarar da suke yi, rahoton The Nation ya tabbatar.

Gwamna Agbu ya samu ƙuri’u 257,926 inda Yahaya ya samu ƙuri’u 202,277 a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga Maris.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi rashin nasara, Kotun daukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar ɗan majalisar jihar Nasarawa

Masu shigar da kara sun shigar da ƙarar ne domin nuna rashin amincewarsu da nasarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta Kefas Agbu suka samu a kan rashin bin ka’idojin dokar zaɓe ta 2022.

Sun kafa dalilan yin aringizon ƙuri'u, lalata takardun sakamakon zaɓe, da kuma tashe-tashen hankula a wasu rumfunan zaɓe.

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tsige Kakakin Majalisa

A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta tsige kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi na jam'iyyar APC.

Kotun ta tabbatar da nasarar ɗan takarar jam'iyyar PDP, Ibrahim Abdullahi Sa'ad a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel