Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar PDP a Arewa

Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar PDP a Arewa

  • Kotun Daukaka Kara ta tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Jamilu Umaru Dahiru Barade
  • Alkalan kotun sun yi umurnin sake zabe a wasu rumfunan zabe a mazabar Bauchi ta tsakiya
  • Dan takarar APC, Aliyu Abdullahi Ilela ne ya kalubalanci nasarar dan majalisar na PDP a kotun

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kwanaki bayan soke zaben kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Kotun Daukaka Kara da ke zama a Abuja, ta sake tsige mataimakin kakakin majalisar, Jamilu Umaru Dahiru Barade na jam'iyyar PDP, rahoton Punch.

Alkalan kotun uku da suka yanke hukunci a ranar Litinin, sun yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta majalisar dokokin jihar Bauchi ta yanke, wadda tun farko ta tabbatar da zaben Barade a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta tsige dan majalisar PDP a jihar arewa, ta daura dan takarar APC a kujerar

Kotu ta tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi
Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar PDP a Arewa Hoto: Court of appeal
Asali: UGC

Saboda haka, kwamitin ya bayar da umarnin sake gudanar da zabe a wasu rumfunan zabe na mazabar, inda mai shigar da kara, Aliyu Abdullahi Ilela na APC, ya yi zargin cewa an kada kuri’u fiye da kima, jaridar Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta bai wa mataimakin kakakin majalisar sannan ta gudanar da sabon zabe a rumfunan zaben da abun ya shafa kafin sanar da wanda ya lashe zaben.

Legit Hausa ta lura cewa hukuncin na zuwa ne yan kwanaki bayan Kotun Daukaka Karar ta tsige kakakin majalisar, Abubakar Suleiman.

Martanin lauyoyin PDP da APC kan hukuncin

Da yake martani ga hukuncin, daya daga cikin lauyoyin mataimakin kakakin majalisar, Barista Aminu Balarabe Isah, ya ce ba a tabbatar da rumfunan zaben da a a sake zaben ba, yana mai cewa saboda karancin lokaci, alkalan sun yi takaitattun bayanai ne kawai kan hukuncin.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci a shari'ar kakakin Majalisa a Kaduna, ta umarci sake zabe

Ya bayyana cewa za a san adadin rumfunan da abun ya shafa da zaran an samu kwafin CTC na hukuncin.

A nashi bangaren, daya daga cikin lauyoyin dan takarar APC, Barista UB Darazo, ya ce hukuncin shine adalci.

Ya ce jam’iyyar APC da dan takararta sun ji dadi da farin cikin wannan hukuncin.

Ya bayyana cewa:

"Hakan alamu ne da ke nuna cewa akwai tangarda a zabukan 2023 a Bauchi."

Kotu ta tsige dan majalisar jihar Neja

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta tsige Hon Suleiman Wanchiko mai wakiltar mazabar Bida I (Arewa) a jihar Neja.

Kwamitin kotun mai mutum uku karkashin jagorancin Mai shari'a Bature Isa-Gafai ya ayyana Bako Kasim na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng