NNPP Ta Yi Rashin Nasara, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ɗan Majalisar Nasarawa

NNPP Ta Yi Rashin Nasara, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ɗan Majalisar Nasarawa

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta kori karar jam'iyyar NNPP da ɗan takararta, ta tabbatar da nasarar ɗan majalisar SDP a jihar Nasarawa
  • Ƙotun ta ce Musa Saidu Gude na SDP ne ya lashe zaben mamba mai wakiltar Uke/Karahi a majalisar dokokin jihar
  • Tuni dai Mista Gude ya sadaukar da wannan nasarar ga ɗaukacin al'ummar mazaɓarsa, ya roƙi yan adawa su maida wuƙar kube

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar mamba mai wakiltar mazaɓar Uke/Karahi majalisar dokokin jihar Nasarawa, Musa Saidu Gude, na jam'iyar SDP.

Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar ɗan majalisar SDP.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar dan majalisar SDP a jihar Nasarawa Hoto: leadership
Asali: UGC

Kotun ta yanke wannan hukunci ne yayin da ta kori ƙarar da jam'iyyar NNPP da ɗan takararta na mazaɓar, Abdulrasheed Haruna, suka ɗaukaka, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Sakkwato

Da yake karanto hukuncin ranar Litinin, shugaban kwamitin alƙalan kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja, mai shari'a J. E. Inayan, ya kori ƙarar bisa rashin cancanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan majalisar ya yi magana bayan samun nasara

A wata hira da ƴan jarida a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, Mista Gude, ya sadaukar da wannan nasara da ya samu ga al'ummar mazaɓarsa.

Ɗan majalisar dokokin ya yi kira ga abokan adawarsa da su taho su haɗa hannu da shi wajen kawo ci gaba ga mazaɓar.

Ya kuma bai wa jama’a tabbacin samun wakilci mai inganci da nagarta a Majalisar Jiha ta hanyar kai kudirori da matsalolin da suka shafi rayuwarsu.

Tun da farko dai kotun sauraron ƙorafe-korafen zabe mai zama a Lafiya ta tabbatar da nasarar ɗan majalisar na SDP kamar yadda INEC ta ayyana a zaben watan Maris.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan karar da ke neman tsige gwamnan PDP

Amma saboda rashin gamsuwa da hukuncin, Haruna ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara, ya nemi a soke zaɓe saboda rashin sanya tambarin NNPP a takardar kaɗa kuri'a yadda ya dace.

Ya kuma yi zargin cewa hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta tafka kura-kurai da saɓa doka a lokacin zaɓen 18 ga watan Maris, rahoton jaridar Pulse.

Shaibu Ya Fara Caccakar Gwamnan PDP Na Edo

A wani rahoton na daban Mataimakin gwamnan Edo ya ce babu tantama zai lallasa duk ɗan takarar da Gwamna Godwin Obaseki yake goyon baya a PDP.

Philip Shaibu, ya bayyana cewa mutanen jihar Edo suna buƙatar nasu ba wanda aka kakaba musu da karfin tsiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262