Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Sake Kwace Kujerar Kakakin Majalisar APC, Ta Tabbatar da Nasarar PDP

Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Sake Kwace Kujerar Kakakin Majalisar APC, Ta Tabbatar da Nasarar PDP

  • Kotun daukaka kara ta sake korar kakakin Majalisa bayan samun shi da tarun zunubai yayin da ake gudanar da zabe
  • Kotun ta kwace kujerar kakakin Majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi na jam'iyyar APC
  • Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar PDP, Ibrahim Abdullahi Sa'ad a matsayin wanda ya lashe zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa - Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben kakakin Majalisar jihar Nasarawa.

Kotun ta rusa zaben kakakin Majalisar jihar, Ibrahim Balarabe Abdullahi na jam'iyyar APC mai wakiltar mazabar Umaisha Ugya.

Kotu ta kwace kujerar kakakin Majalisar jihar Nasarawa, ta bai wa PDP
Kotun daukakak kara ta yi hukunci kan shari'ar kakakin Majalisar Nasarawa. Hoto: Court of Appeal.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Nasarawa?

Kotun da ke zamanta a birnin Tarayya Abuja ta kuma tabbatar da nasarar dan takarar PDP, Ibrahim Abdullahi Sa'ad a Majalisar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yanzu: Kotun daukaka kara ta tsige mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar PDP a arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, kotun ta ce dan takarar jam'iyyar PDP, Abdullahi shi ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris ba tare da wata jayayya ba.

Wannan na zuwa ne yayin da kakakin Majalisar ke takun saka da Daniel Ogazi da ke wakiltar mazabar Kokona ta Gabas.

Mene ke faruwa a Majalisar kan shugabanci?

'Yan Majalisar na takun saka ne kan shugabancin Majalisar tun bayan nada Mista Balarabe Abdullahi a matsayin shugaban Majalisar.

Daily Trust ta tattaro cewa rikicin neman shugabancin Majalisar ya haifar da kasancewar shugabanni biyu a kwanakin baya.

Har ila yau, kotun daukaka kara ta raba gardama a shari'ar zaben Majalisar jihar Bauchi.

Kotun ta kwace kujerar Abubakar Sulaiman a ranar Juma'a inda ta ce Suleiman ya ci a mazabar Ningi ta Tsakiya wacce ke cike da kura-kurai.

Kara karanta wannan

Shari’ar Gwamna: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar APC, Ta Tabbatar da Nasarar PDP

Kotu ta yi hukunci a zaben kakakin Majalisar Gombe

A wani labarin, kotun daukaka kara ta raba gardama a shari'ar zaben kakakin Majalisar jihar Gombe.

Kotun ta tabbatar da nasarar Abubakar Luggerewo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Akko ta Tsakiya a jihar.

Har ila yau, kotun ta yi watsi da karar dan jam'iyyar PDP, Bashir Gaddafi wanda karamar kotun ta ba shi nasara yayin hukuncinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel