Kotun Koli Ta Kori Karar da Sanata Adeyemi Ya Shigar da Ododo Kan Zaben Jihar Kogi

Kotun Koli Ta Kori Karar da Sanata Adeyemi Ya Shigar da Ododo Kan Zaben Jihar Kogi

  • Kotun ƙoli ta kori karar da Sanatan Adeyemi ya kalubalanci nasarar Ahmed Ododo a zaben fidda gwanin APC a jihar Kogi
  • A zaman yanke hukunci ranar Litinin, Kotun ta yi fatali da ƙarar ne saboda rashin cancanta, ta kuma ci tarar mai ƙara
  • Ahmed Usman Ododo ne ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC na zaben gwamnan jihar Ƙogi mai zuwa a watan Nuwamba

FCT Abuja - Kotun ƙolin Najeriya ta sanar da hukuncinta kan ƙarar da Sanata Smart Adeyemi mai wakiltar Kogi ta yamna ya shigar kan zaɓen fidda gwanin APC.

Ƙotun Allah ya isa kamar yadda ake mata laƙabi ta kori ƙarar da Sanatan ya kalubalanci sahihancin sakamakon zaben fidda ɗan takarar gwamnan APC a jihar Kogi, Dailytrust ta ruwaito.

Alhaji Usman Ododo.
Kotun Allah ya isa ta raba gardama kan tikitin APC a jihar Kogi Hoto: Ahmed Usman Ododo
Asali: Twitter

A hukuncin da kwamitin alƙalai uku na Kotun suka yanke da murya ɗaya ta bakin mai shari'a Emmanuel Agim, ranar Litinin, Kotun ta kori ƙarar ne saboda rashin cancanta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Dage Sauraron Daukaka Karar Atiku, Peter Obi, Ta Yi Watsi da Karar APM

"Gaɓa ɗayan karar, wannan karar da aka ɗaukaka ta gaza saboda ba ta cancanta ba," in ji Alkalin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeyemi ya kalubalanci zaben fidda gwanin APC wanda ya ayyana Ahmed Usman Ododo a matsayin ɗan takarar gwamna a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba.

Sai dai Kotun ƙolin ta bayyana cewa Sanata Adeyemi ya gaza gamsar da cewa hukuncin da Kotunan baya suka yanke bayan gudanar da bincike, kuskure ne.

Bayan haka kwamitin alƙalan ya ci tarar wanda ya shigar da ƙara kuɗi Naira miliyan biyu wanda za a bai wa Ododo da kuma jam'iyyar APC.

Yadda shari'ar ta faro tun daga farko

Tun da farko, Sanata Adeyemi ya roƙi babbar Kotun tarayya, a ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/556/2023, ta ayyana zaben fidda gwanin da APC ta yi a matsayin wanda ya saɓa doka.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Dalilai 4 da Ka Iya Sanyawa APC Ta Sha Kashi a Jihar Kogi

Ya kuma jaddada cewa jam'iyyar APC ba ta gudanar da zaɓen fidda ɗan takara ba kamar yadda doka ta tanada, amma a ranar 12 ga watan Yuli, mai shari'a James Omotosho, ya yi fatali da ƙarar.

Bayan haka kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta aminta da wannan hukuncin kana ta kori ƙarar da Sanatan ya ɗaukaka, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Hotunan yadda aka cika gidan Kwankwaso

A wani rahoton kuma Mahaddatan Alkur'ani mai girma sun cika maƙil a gidan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso da ke Bampai ranar Litinin

Sun je gidan ne domin neman gurbin shiga sabuwar makarantar Islamiyya da Boko, wacce Kwankwaso ya ce zasu horar da Almajirai, mun haɗa muku Hotuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel