Zaben Kogi: Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa AA

Zaben Kogi: Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa AA

  • Jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta a jihar Kogi yayin da zaɓen gwamna ke ƙara kusantowa a wata mai zuwa
  • Yahaya Ododo, ya yi murabus daga mamban jam'iyyar APC, kana ya koma AA domin mara wa ɗan takarar jam'iyyar baya
  • Ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da daidaito, gaskiya da adalci a kujerar gwamnan jihar Kogi

Jihar Kogi - Wani babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga ƙaramar hukumar Ankpa ta jihar Kogi, Yahaya Ododo, ya sauya sheƙa zuwa Action Alliance (AA).

Jaridar The Cable ta tattaro cewa wannan na zuwa ne yayin da rage wata ɗaya gabanin zaɓen gwamma wanda za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Tsohon jigon APC a Kogi, Yahaya Ododo.
Zaben Kogi: Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa AA Hoto: punchng
Asali: UGC

Ɗan siyasan ya bayyana cewa ya yanke shawarar koma wa jam'iyyar AA ne domin tabbatar da daidaito, gaskiya da adalci a kujerar gwamnan jihar Kogi, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Ƙara Yi Wa Jam'iyyun APC da Labour Party Babban Lahani Ana Dab Da Zabe

Yahaya Ododo ya faɗi haka ne a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja, babban birnin jihar da safiyar ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A nasa jawabin, Omale, wani babban soja ne mai ritaya, ya ce gwamnati mai ci ta hau karagar mulki ne bisa akasi, inda ya nuna cewa lokaci ya yi da Kogi ta Yamma zata samar da gwamna.

Ɗan takarar AA shi ne a sahun gaba - Omale

A cewarsa, cikin dukkan ‘yan takarar gwamna, Otunba Braimoh ne kadai ke da tarin kudirorin da zai iya fitar da jihar daga kangin talauci da ya dabaibaye ta tsawon shekaru.

A kalamansa ya ce:

"Na jima ana damawa da ni a siyasar jihar Kogi tsawon shekaru, na yi aiki da tsohon ministan shari'a kuma Antoni Janar, Bayo Ojo, da tsohon shugaban ma'aikatan shugaban ƙasa, Olushola Akanmode."

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Da Wasu Manyan Shugabannin Mata Sun Ƙara Ruguza Jam'iyyar PDP a Arewa

"Jam'iyyar AA na ci gaba da karɓan masu sauya sheƙa daga jam'iyyu daban-daban ciki harda jigon PDP a gundumar Ojoku, Honorabul Samuel Omale, tare da ɗumbin magoya bayansa."
"Haka kuma, wasu mambobin APC sun koma AA, inda suka ce a shirye su ke wajen ganin sun taimaka an tabbatar da shirin samar da wadata na dan takarar gwamna."

"Akwai Babban Abin Damuwa" INEC Ta Bayyana Abinda Ta Hango Zai Kawo Cikas a Zaɓen Gwamnoni 3

A wani rahoton na daban INEC ta ce yanayin tsaro da rikici tsakanin jam'iyyun siyasa babban abin damuwa ne a zaɓukan Imo, Kogi da Bayelsa.

Kwamishinan yaɗa labaran INEC na ƙasa, Mista Sam Olumekun, ya ce zasu ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel