Edo da Jihohin 4 da Ake Fama da Rashin Jituwa tsakanin Gwamna da Mataimaki

Edo da Jihohin 4 da Ake Fama da Rashin Jituwa tsakanin Gwamna da Mataimaki

  • Hope Uzodinma ba zai shiga takara da Placid Njoku a zaben gwamnan Imo, ya canza ‘yar takarar mataimakiyar Gwamna
  • Abubuwa sun yi muni tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da Phillip Shu’aibu wanda ya ke ta harin kujerarsa a jihar Edo
  • Tun da Gwamna Rotimi Akeredolu ya dawo daga jinya daga kasar waje, take-take su ka nuna za a kori Lucky Aiyedatiwa

Abuja - Akwai jihohin kasar nan da aka samu sabanin shugabanci tsakanin gwamnoni da mataimakansu, hara bin ya yi kamari.

Rahoton nan ya tattaro jihohin da ake zargin abubuwa ba su tafiya daidai tsakanin Mai girma Gwamna da kuma mataimakinsa.

A wasu jihohin, masu mulki sun karyata zargin da ake yi, da alama kokarin rufa-rufa ne.

Gwamna da Mataimaki
Gwamnan jihar Imo da Gwamnan jihar Kogi Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: Twitter

1. Gwamna Jihar Imo

Mai girma Hope Uzodinma ya yi watsi da Placid Njoku a takarar da ya ke yi wannan karo, ya canza abokin neman takararsa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 Na Arewa Sun Gana a Katsina, Sun Cimma Matsaya Kan Muhimman Abu 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A maimakon Njoku mai shekara 76, Gwamna Uzodinma ya na so Nnedinma Ekomaru ta zama mataimakiyar gwamna idan ya lashe zabe.

2. Jihar Ondo

A jihar Ondo kuwa abin da ya yi zafi, a matsayinsa na mataimakin Gwamna, Lucky Aiyedatiwa, ya gagara hana a iya tunbuke shi.

Alamu sun nuna alakar Aiyedatiwa da Rotimi Akeredolu ta zo karshe tun da Gwamnan ya warke, ‘yan majalisar dokoki na yunkurin yin waje da shi.

3. Jihar Edo

Kowa ya ga yadda dangantakar Godwin Obaseki da Phillip Shu’aibu ta yi tsami, har sai da ta kai mataimakin Gwamna ya bar gidan gwamnati.

Kwanakin baya jami’an tsaro su ka haka Phillip Shu’aibu ganin Mai gidansa. Daga baya ya nemi afuwa, ya na kuma harin kujerar Gwamna a badi.

4. Jihar Kogi

Kamar dai a Edo, Edward Onoja ya yi wa mai gidansa biyayya a zabukan baya, da ya nemi zama magajinsa, sai abubuwa su ka canza a jihar.

Kara karanta wannan

Abba Kabir Ya Bai Wa Matashin Da Ya Dawo Da N15m Yayin Aikin Hajji Kujerar Makka, Aiki, Ya Masa Goma Ta Arziki

Edward Onoja ya nuna har yau babu barakar da ta ke tsakaninsa da Yahaya Bello, sai dai Gwamnan bai goyi bayansa a zaben ‘dan takara ba.

Tinubu ya yi nadin mukamai

Idris Alubankudi Saliu ya shiga rukunin wadanda za su rika ba shugaban Najeriya shawara kamar yadda rahoto ya fito a yammacin Laraba.

Shekaru kimanin 20 kenan da Idris Alubankudi Saliu ya fito, ya yi karatunsa ne a jami’ar Amurka, matashin ya yi suna a fasahar zamani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel