Abba Gida Gida Ya Bai Wa Matashin Da Ya Dawo Da N15m Yayin Aikin Hajji Kujerar Makka, Aiki

Abba Gida Gida Ya Bai Wa Matashin Da Ya Dawo Da N15m Yayin Aikin Hajji Kujerar Makka, Aiki

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bai wa matashin da ya mayar da makudan kudade da ya tsinta yayin aikin hajji aiki a hukumar
  • Matashin Dayyabu Haladu wanda ma’aikacin wucin gadi ne a hukumar Alhazai ya mayar da kudade miliyan 15 bayan ya tsinta
  • Gwamnan ya kuma masa alkawarin kujerar aikin hajji bayan ba shi kyautar Naira miliyan daya saboda kyakkyawan hali da ya nuna

Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bai wa matashin da ya mayar da Dala dubu 16 da ya tsinta yayin da ake aikin hajji aiki a hukumar.

Dayyabu Haladu wanda ke aiki a Hukumar Alhazai a jihar na wucin gadi, an ba shi aiki na din-din-din da kuma yautar Naira miliyan daya.

Abba Kabir ya bai matashi kyautar kujerar Hajji da aiki
Abba Gida Gida yayin da ya ke mika kyautar ga matashin. Hoto: TheCable.
Asali: Facebook

Meye Abba Kabir ya ce kan matashin?

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo Ga Matasa Yayin Da Tinubu Ya Yi Alkawarin Samar Da Ayyuka 500,000, Ya Yi Karin Bayani

Gwamna Abba Kabir shi ya bayyana yayin karbar rahoton hukumar na aikin hajjin shekarar 2023, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Dayyabu wanda aka fi sani da Dan Gezawa ya samu kyautar kujerar Makka wanda za a yi nan gaba.

Ya kara da cewa abin da Dayyabu ya aikata ya nuna irin yadda ya ke da wadatar zuci inda ya ce tabbas halayensa abin koyi ne ga sauran al’umma.

Ya ce:

“A matsayinsa na ma’aikacin wucin gadi wanda albashinsa bai taka kara ya karya ba, amma ya yi kokarin dawo da fiye da miliyan 15 da ya tsinta.
“Ya nuna yadda wannan bawan Allah ke tsoron ubangiji kuma ya kamata ayi alfahari da shi.”

Gwamnan ya bukaci 'yan jihar da su ci gaba da daukaka sunan jihar wurin nuna kyawawan halaye don rayuwa cikin farin ciki.

Kara karanta wannan

Sharri Ake Yi Mani: Ban Goyi Bayan Atiku a Boye a Zaben 2023 ba – Jigon APC

Wane martani matashin ya yi kan kyautar Abba Kabir?

A martaninshi, Dayyabu ya ce ya mayar da kudaden ne ga hukumar Alhazai saboda tsoron Allah.

Ya ce bai kamata mutum ya dauki abin da ba na shi ba duk cikin halin kunci da ya ke ciki.

Ya godewa gwamnan kan irin wannan kyauta da ya ba shi inda ya ce wannan shi ne abu mafi farin ciki a rayuwarsa.

Gwamna Abba Kabir ya kuma yi alkawarin karrama direban adaidaita sahu da ya dawo da miliyan 16 da aka manta a kekensa, The Guardian ta tattaro.

Majalisar Kano ta bai wa direban adaidaita sahu kyautar N1.5m

A wani labarin, majalisar dokokin jihar Kano ta bai wa Auwalu Salisu Naira miliyan 1.5 saboda kyakkyawan hali da ya nuna.

Auwalu, direban adaidaita sahu shi ne ya mayar da Naira miliyan 15 ga wani dan Chadi da ya manta a cikin adaidaita sahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel