Katsina: Gwamnonin Arewa Ta Yamma Sun Hadu Don Magance Matsalar Tsaro da Noma

Katsina: Gwamnonin Arewa Ta Yamma Sun Hadu Don Magance Matsalar Tsaro da Noma

  • Gwamnoni 6 na jihohin Arewa maso Yamma sun zauna a gidan gwamnatin Katsina kan batutuwan da suka addabi yankinsu
  • Yayin taron ranar Talata, sun cimma matsayar cewa zasu yi aiki tare wajen magance matsalar tsaro da bunƙasa noma
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya jinjina wa shugaban ƙasa Tinubu bisa aikin da ya sa hannu na samar da wutar lantarki

Jihar Katsina - Gwamnonin jihohin shiyyar Arewa maso Yamma sun kuduri aniyar yin aiki tare domin magance kalubalen rashin tsaro da inganta harkar noma a yankin.

Gwamnonin sun cimma wannan matsaya ne a yayin wani muhimmin taro da suka gudanar a ranar Talata a gidan gwamnatin jihar Katsina, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamnonin Arewa maso Yamma sun yi zama a Katsina.
Katsina: Gwamnonin Arewa Ta Yamma Sun Hada Don Magance Matsalar Tsaro da Noma Hoto: thecable, Isah Miqdad
Asali: Twitter

Taron ya samu halartar Malam Dikko Radda, gwamnan jihar Katsina, Abba Ƙabir Yusuf na jihar Kano, Dauda Lawal na jihar Zamfara da Kauran Gwandu na jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yunƙuro, Ya Kaddamar da Sabuwar Rundunar Tsaro Domin Kawo Karshen 'Yan Bindiga

Sauran sun ƙunshi Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato da mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Aminu Usman, wanda ya wakilci gwamna Umar Namadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da Sanusi Tofa, babban sakataren yada labarai na gwamna Radda ya fitar, gwamnonin sun ce zasu yi aiki tare ne domin ci gaban yankin.

Muhimman abubuwan da suka amince a taron

Gwamnonin sun ce dukkansu sun amince za su yi aiki tare don inganta harkar noma ta hanyar dabarun zamani da kuma samar da kayayyaki da kasuwanni.

Har ila yau, sun amince da tsara hanyar samar da ci gaban tattalin arzikin yankin yadda ya dace, ta hanyar yin amfani da albarkatun kasa, na zahiri da na dan Adam da Allah ya albarkaci jihohinsu.

Sanarwar ta ruwaito Abba Ƙabir Yusuf, gwamnan Kano, yana jinjina wa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan aikin samar da wutar lantarki a jihohin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Samu Mukami Mai Muhimmanci

Abba ya ce:

"Muna amfani da wannan dama wajen yaba wa Tinubu bisa yadda ya tsoma hannu a aikin samar da wutar lantarki a jihohin Arewa maso Yamma da nufin bunkasa tattalin arzikinsu da samar da karin ayyukan yi."

Ya Zama Wajibi Shugaba Tinubu Ya Bayyana Ainihin Bayannasa, Peter Obi

A wani rahoton kuma Peter Obi ya ce taƙaddama kan ainihin takardun bayanan BolaɓTinubu abin kunya ne ga Najeriya a idon ƙasashen duniya.

Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a zaɓen 2023 na LP ya buƙaci shugaban ƙasa ya fito ya bayyana gaskiya kan haƙiƙanin bayanansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel