Kwamitin Bincike: Sakataren PDP Ya Maida Babbar Mota Ga Gwamnatin Sokoto

Kwamitin Bincike: Sakataren PDP Ya Maida Babbar Mota Ga Gwamnatin Sokoto

  • Umar Bature, Sakataren tsare-tsaren jam'iyyar PDP ta ƙasa ya maida motar Tarakta ga gwamnatin jihar Sakkwato
  • Ya ce tsohuwar gwamnatin Aminu Tambuwal da ta shuɗe ce ta ba shi hayar motar amma sai da ya mata gyara kafin ta fara aiki
  • Hukumar shari'a ta musamman da gwamna Ahmad Aliyu ya kafa domin binciken gwamnatin Tambuwal ta ɗage zamanta

Jihar Sokoto - Sakataren tsare-tsare na PDP ta ƙasa, Umar Bature, ya maida motar Tarakta wacce tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe a jihar Sakkwato ta ba shi haya.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Bature ya faɗi haka ne a wurin zaman hukumar da Gwamna Ahmad Aliyu ya kafa domin binciken ayyuna Aminu Waziri Tambuwal.

Taswirar jihar Sakkwato.
Kwamitin Bincike: Sakataren PDP Ya Maida Babbar Mota Ga Gwamnatin Sokoto Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A ci gaban da zaman hukumar ranar Alhamis, Bature, tsohon kwamishinan albarkatun ruwa, ya ce ma’aikatar noma ce ta ba shi hayar tarakta a lokacin yana kwamishina.

Kara karanta wannan

Babbar Matsala 1 Da Aka Gano Bayan Taron da Atiku Ya Gudanar Kan Shugaba Tinubu a Abuja

A ruwayar Leadership, Bature ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Marigayi kwamishinan noma, Muhammad Arzika Turata, ya tambayi mambobin majalisar zartarwa ta jiha a lokacin ko akwai mai sha’awar noma domin akwai taraktocin da za a bada haya."
"Nan take da nun sha'awa kuma aka bani guda ɗaya. Ni na gyarata, na canza tayoyi kuma na yi wa injinta sabis. Kwanan nan na ƙara canja tayoyi."
"Lokacin da na sauka a 2021, na so mayar da motar amma suka ce na barta a wurina har sai sun nemi hakan. Yayin da na samu sammacin kwamiti ranar 23 ga watan Satumba, na maida Taraktar ranar 26 ga watan."
"A ranar 29 ga Satumba, na samu takardar amincewa daga ma’aikatar kan maida motar Tarakta,” inji shi.

Nan take aka amince da takardar da ya gabatar, kana shugaban Hukumar, Mai Shari’a Mu’azu Pindiga ya dage zaman har zuwa ranar 7 ga watan Oktoba domin ci gaba daga inda aka tsaya.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Fara Raba Wa Talakawan Jiharsa Kuɗi N5,000 Duk Wata Don Rage Musu Radaɗi

Gwamna Abidoun Ya Ɗauki Sabbin Malamai 1,000 Aiki a Gwamnatin Ogun

A wani rahoton kuma Gwamna Dapo Abiodun ya ce gwamnatinsa ta ɗauki sabbin malamai 1,000 aiki a makarantu gwamnati na jihar Ogun.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa akwai sabbin gyare-gyare da zai yi wa ɓangaren ilimi wanda ya ƙunshi ɗaukar malamai masu neman kwarewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel