Gwamnatin Jihar Ekiti Ta Fara Raba Wa Talakawa N5,000 Duk Wata

Gwamnatin Jihar Ekiti Ta Fara Raba Wa Talakawa N5,000 Duk Wata

  • Gwamnatin jihar Ekiti ta fara raba tallafin N5,000 ga talakawa 7,000 da ke jihar da nufin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur
  • Kwamishinan yaɗa labarai, Taiwo Olatunbosun, ya ce Gwamnatin Biodun Oyebanji zata ƙara yawan masu cin gajiyar tallafin zuwa 10,000
  • Ya kuma buƙaci waɗanda zasu riƙa karɓan tallafin na tsawon watanni biyar su yi amfani da shi ta hanyar da ya dace

Jihar Ekiti - Gwamnatin jihar Ekiti ƙarƙashin jagorancin Gwamna Biodun Oyebanji ta fara bayar da Naira 5,000 kowane wata ga mabukata 7,000 a jihar.

Gwamnatin ta ce biyan kudin zai ci gaba na tsawon watanni biyar ne a wani mataki na dakile tasirin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti.
Gwamnatin Jihar Ekiti Ta Fara Raba Wa Talakawa N5,000 Duk Wata Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Mista Taiwo Olatunbosun, shi ne ya bayyana haka a Ado-Ekiti, babban birnin jihar ranar Laraba, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kuma Ku Dana: Gwamnan APC Mai Shirin Barin Mulki Ya Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci

Ya kuma nanata kudirin gwamnatin Gwamna Biodun Oyebanji na rage radadin talauci da inganta rayuwar al’umma a Jihar, musamman ma wadanda suka fi kowa rauni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olatunbosun ya kara da cewa nan ba da dadewa ba za a fara raba wa ƙarin wasu marasa galihu guda 3,000 tallafin Naira 5,000 ga kowane mutum na tsawon watanni biyar.

Hakan zai sa waɗanda ke samun tallafin su zama jimillar mutane 10,000 kuma daga nan zuwa ƙarshen shirin kowane mai cin gajiyar zai karɓi Naira 25,000.

Jerin mutane da ake bai wa tallafin

Ya yi bayanin cewa waɗanda zasu amfana 10,000 daga dukkan ƙauyukan jihar an zaƙulo su ne a cikin rajistar ma’aikatar kasafin kudi, tsare-tsaren tattalin arziki.

Kwamishinan ya ce rukunonin wadanda zasu ci gajiyar shirin sun hada da “masu nakasa 559; zawarawa 3,065; Dattawa 1,101 da suka haura shekara 65, matasa 1,153 waɗanda aƙalla mutum ɗaya ya dogara da su."

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

Ya bukaci masu cin gajiyar tallafin da su yi amfani da kuɗaɗen ta hanyar da ya dace don rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da inganta rayuwarsu, Guardian ta rahoto.

Gwamna Diri da Ya Dawo da Ma'aikata 704 da Aka Kora a Manyan Makarantun Jihar Bayelsa

A wani rahoton na daban Gwamna Diri ya maida ma'aikata sama da 700 da aka kora daga manyan makarantun jihar Bayelsa guda uku.

A wata sanarwa da sakataren watsa labaransa ya fitar, Douye Diri ya ce matakin maida su bakin aiki zai fara aiki daga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel