Zaben Gwamnan Kano: Jam'iyyar NNPP Ta Magantu Kan Zanga-Zangar Adawa Da APC a Landan

Zaben Gwamnan Kano: Jam'iyyar NNPP Ta Magantu Kan Zanga-Zangar Adawa Da APC a Landan

  • Jam'iyyar NNPP ta ce wadanda suka yi zanga-zanga a Ofishin Jakadancin Birtaniya a Landan a ranar bikin yancin kasa yan Najeriya ne masu kishin kasa
  • Wasu yan Najeriya sunyi zanga-zanga a Landan kan hukuncin zaben gwamnan Kano; wasu da suke kira kansu masu ruwa da tsaki na APC sun soke su
  • A cikin sanarwa da ya fitar, Kakakin NNPP, Barista Ladipo Johnson, wanda Legit ta samu, jam'iyyar ta ce abin da masu zanga-zangan suka yi nuna rashin gamsuwa bisa 'rashin adalci'

Landan, Birtaniya - Jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP) ta soke zargin cewa ita ta dauki nauyin wadanda suka yi zanga-zanga a Ofishin Jakadancin Birtaniya a ranar 1 ga watan Oktoba (ranar yancin Najeriya).

Jam'iyyar NNPP ta ce masu zanga-zangan yan Najeriya ne 'masu kishin kasa' da ke zaune a kasashen waje kuma sun nuna rashin gamsuwarsu ne kan hukuncin Kotun Zaben gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Zama Shugaban Najeriya Na Farko Da Kotun Koli Za Ta Tsige – Hadimin Atiku

NNPP ta yi magana kan zanga-zangar Landan
Yan Najeriya a kasar waje sun tafi ofishin jakadancin Birtaniya a Landan sunyi zanga-zanga kan hukuncin zaben gwamnan Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Nasir Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

Wadanda suka yi zanga-zanga a Landan yan Najeriya ne masu kishin kasa: NNPP

Idan za a iya tunawa wata kungiya wacce ke goyon bayan jam'iyyar APC ta soke zanga-zangar da aka yi a Landan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke martani a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, Kakakin NNPP, Barista Ladipo Johnson, ya musanta wannan zargin.

Kamar yadda Vanguard ta rahoto, Johnson, cikin wata sanarwa ya ce masu zanga-zangar masu kishin kasa ne.

Wani sashi na kalamansa ya ce:

"Zanga-zangar da wadannan masu kishin Najeriyan suka yi ya nuna wa kasashen duniya cewa kotun Najeriya na bukatar taimako domin ta zama mai cin gashin kanta.
"Akasin sukar da APC ta yi, masu zanga-zangar a wannan matakin sun nuna hakan ne a maimakon fada da bangaren shari'a ko wata hukuma ta gwamnati."

Kara karanta wannan

Kano: DSS Ta Kama Matar da Ta Yi Barazanar Kashe Mataimakin Tinubu, Gawuna da Alƙalai a Bidiyo

Kotu ta soke nasarar Gwamna Yusuf na Kano

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa kotun sauraron karar zaben gwamnan jihar Kano ta tsige Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamna, ta kuma ayyana Nasiru Gawuna jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.

Hukumar Zabe ,INEC, ta ayyana Yusuf, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, a matsayin wanda ya ci zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164