Karin Bayani: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna
- Kotun zaben gwamnan jihar Kaduna ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sanin a jam’iyyar APC a zaben 2023
- Kotun zaben ta yi fatali da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Isah Ashiru suka shigar na kalubalantar nasarar Uba Sani
- Kwamitin kotun zaben karkashin mai shari'a Victor Oviawe ya yanke hukunci ta manhajar Zoom a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kaduna ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani, rahoton Daily Trust.
Da yake yanke hukunci kan karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru, suka shigar don kalubalantar nasarar Gwamna Uba Sani, kwamitin kotun ya riki cewa Sani ne zababben gwamna.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Sani, wanda yay i takara a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris.
Ashiru da jam’iyyarsa sun ki amincewa da sakamakon inda suka nufi kotu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin mai shari'a Victor Oviawe ya yanke hukunci ta manhajar Zoom ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba.
Gwamna Uba Sani ya yi martani kan hukuncin kotun zabe
Uba Sani ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook inda yake tabbatar da nasararsa a kotun zaben.
Ya ce:
"“Na yi matukar farin ciki da kuma kankan da kai ga hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke na tabbatar da nasarar da na samu a zaben Gwamnan Jihar Kaduna a 2023.
“Hukuncin ya tabbatar da yawan kuri’un da mutanen jihar Kaduna masu karamci suka bani.
“Na yaba wa kotun kan tsayin dakan da suka nuna. Sun inganta bangaren shari'armu da tsarin dimokuradiyyar zabe."
Jira Ya Kare: Kotu Ta Bayyana Ranar Da Za Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Nasarar Babban Gwamnan APC a Zabe
Ogun: Kotun zabe za ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar a ranar Asabar
A wani labarin, mun ji cewa k otun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ogun da ke zamanta a Abeokuta, ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar gwamna na jam'iiyyar PDP, Ladi Adebutu, ya shigar kan Gwamna Dapo Abiodun.
Jaridar Nigerian Tribune ta kawo rahoto cewa kotun ta bayyana cewa za ta yanke hukuncinta kan shari'ar a ranar Asabar, 30 ga watan Satumban 2023.
Asali: Legit.ng